Ana Tsaka da Zanga Zanga, ECOWAS Ta Yi Maganar Bude Iyakokin Kasashe

Ana Tsaka da Zanga Zanga, ECOWAS Ta Yi Maganar Bude Iyakokin Kasashe

  • Kungiyar hadin kan kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) ta yi magana kan bude iyakokin kasashen Nijar da Benin
  • Shugaba mai kula da harkokin kasuwanci na ECOWAS, Dakta Muhammad Ibn Chambas ne ya yi bayanin a yau Alhamis
  • Dakta Muhammad Chambas ya bayyana amfani da za a samu wajen habaka tattali idan aka bude iyakokin kasashen biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar ECOWAS ta bukaci kasashen Nijar da Benin su koma teburin sulhu domin bude iyakokinsu.

Shugaban harkar kasuwanci a kungiyar ECOWAS, Dakta Muhammad Chambas ne ya yi kiran a Abuja.

ECOWAS
ECOWAS ta bukaci a bude iyakokin Nijar da Benin. Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Dakta Muhammad Chambas ya bayyana amfanin da za a samu idan kasashen suka bude iyakokinsu.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta koma fitina: An kashe mutum 1 yayin da aka babbake gidan mai a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka rufe iyakokin kasashen?

Rahotanni sun nuna cewa tun a watan Yulin shekarar 2023 aka rufe iyakokin kasashen Nijar da Benin saboda wani sabani da suka samu a tsakaninsu.

A shekarun baya kasashen sun kasance suna ƙawance ta bangarori da dama kuma ana harkokin kasuwanci da tafiye tafiye ta iyakokinsu.

Amfanin bude iyakoki ga yankin Afrika

Dakta Muhammad Chambas ya bayyana cewa idan aka bude iyakokin za a samu sauƙin zirga zirga a tsakaninsu.

Muhammad Chambas ya kara da cewa za a samu sauki a harkar kasuwancin ƙasashen da sauran ƙasashen da ke makwabtaka da su.

Kiran Chambas ga Nijar da Benin

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Dakta Muhammad Chambas ya yi kira ga shugaban Nijar da Benin kan sake zama domin duba bude iyakokin kasashen.

Chambas ya ce ya kamata Nijar da Benin su duba 'yan uwantaka na Afirka da ECOWAS da ya hada su wajen yin gaggawar bude iyakokin.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi, yan sanda sun cafke matashin da ya fito zanga zanga

ECOWAS ta dage takunkumi ga kasashe

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta dage takunkumin da ta sakawa Jamhuriyar Nijar da sauran kasashen da sojoji ke mulki.

Hasashe kan rahotanni daga taron da ECOWAS ta yi a baya-bayan nan sun nuna cewa an dage takunkumi guda takwas ga dukkan kasashen.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng