Mahaifiyar Fitaccen Ɗan Wasan Ƙwallon Duniya, Pele, Ta Rasu Tana da Shekara 101

Mahaifiyar Fitaccen Ɗan Wasan Ƙwallon Duniya, Pele, Ta Rasu Tana da Shekara 101

  • Mahaifiyar fitaccen dan wasan kwallon kafa na Brazil, Pele, ta mutu a kasar Brazil tana da shekaru 101 bayan fama da jinya
  • Gidauniyar Pele ta sanar da da labarin mutuwar Celeste Arantes yayin da ta bayyana jimami da kuma keyar mahaifiyar dan kwallon
  • Ko a karshen shekarar 2022 da Pele ya rasu, mahafiyarsa Arantes ba ta sani ba saboda halin jinya da kuma tsufa da take ciki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Brazail - Celeste Arantes, mahaifiyar fitaccen dan wasan kwallon kafa na Brazil, Pele, ta rasu a ranar Juma'a tana da shekaru 101. Pele ya mutu watanni 18 kafin mutuwar Celeste.

Wadda aka haifa a ranar 23 ga Oktoba, 1940, Arantes ta haifi Pele ta na da shekaru 17 kacal, yaron da ya zama dan kwallon kafa da ake kallo matsayin mafi kwarewa a duniya.

Kara karanta wannan

Ana cikin rigimar sarautar Kano, miyagu sun yi ta'asa har da jikkata yan sanda

Mahaifiyar Pele ta rasu a Brazil
Mahaifiyar fitaccen dan wasan kwallon kafa, Pele, ta mutu tana da shekara 101. Hoto: Pelé Foundation
Asali: Instagram

Mahifiyar Pele ta rigamu gidan gaskiya

Gidauniyar Pele ta sanar da da labarin mutuwar Celeste Arantes a shafinta na Instagram duk da cewa ba a bayyana dalilin mutuwar nata ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Arantes ta shafe shekaru biyar da suka gabata a cikin yanayin jinya, abin da ya sa kenan ba a sanar da ita mutuwar ɗanta ba a karshen shekarar 2022.

Wata sanarwa da hukumar kwallon kafar Brazil ta fitar ta ce Celeste Arantes ta yi jinyar kwana takwas a asibiti kafin mutuwarta, kamar yadda rahoton API ya nuna.

Gidauniyar Pele na kewar Celeste Arantes

Gidauniyar ta Pele ta bayyana cewa mahaifiyar dan wasan kwallon daya tilo da ya lashe gasar cin kofin duniya sau uku ta kasance abin koyi ga jama'a.

"“Abuwan da muke ji game da mutuwar ‘Celestinha,’ na da yawa. Yayin da muke kewarta, a hannu daya kuma muna matukar alfari da zamanta a rayuwarmu."

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, fitaccen Sarki mai daraja ya riga mu gidan gaskiya a Landan

- In ji Gidauniyar Pele.

Duba sanarwar a nan kasa:

Fitaccen ɗan ƙwallo, Pele, ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen ‘dan kwallon kafa na kasar Brazil, Pele, ya mutu yana da shekaru 82 a duniya kamar yadda iyalansa suka sanar.

An ce Pele ya rasu ne yammacin ranar Alhamis, 29 ga watan Disambar 2022, kuma ba a sanar da mahaifiyarsa labarin mutuwar tasa ba saboda halin da take ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.