Taka leda: Pele ya ce ko kadan Messi bai kama kafarsa a iya kwallon kafa ba

Taka leda: Pele ya ce ko kadan Messi bai kama kafarsa a iya kwallon kafa ba

- Pelé, ya bayyana cewa ya zarce iyawar dan wasan da ya lashe kambun Ballon d'Or har sau biyar, Lionel Messi, don haka batun a rinka hadasu ma bai taso ba

- Pele ya ce, Lionel Messi, "na da bajinta ne kawai", kuma hatta ma takwaransa dan kasar Argentina, Diego Maradona ya zarce shi a wasan taka leda

- Ya yi nuni da cewa mai iya gogayya da Pele sai wanda ya san sirrin dukan kwallo da kafar hagu da dama, kuma ya iya zura kwallo a raga da kai

Shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya, Edson Arantes do Nascimento, wanda aka fi sani da Pelé, ya bayyana cewa ya zarce iyawar dan wasan da ya lashe kambun Ballon d'Or har sau biyar, Lionel Messi, don haka batun a rinka hadasu ma bai taso ba.

Pele ya ce, Lionel Messi, "na da bajinta ne kawai", kuma hatta ma takwaransa dan kasar Argentina, Diego Maradona ya zarce shi a wasan taka leda.

Pele ya yi nuni da cewa Messi mai shekaru 31 na da kaifi daya ne mai saurin ganewa, wanda yafi taka leda da kafar hagunsa, don haka bai kamata a rinka hada iyawarsa da ta shahararru a taka ledar ba, wadanda har suka gama ba a iya gane gabansu.

KARANTA WANNAN: Debo ruwan dafa kai: Wani saurayi ya kashe budurwarsa tare da binne gawarta a dakinsa

Taka leda: Pele ya ce ko kadan Messi bai kama kafarsa a iya kwallon kafa ba
Taka leda: Pele ya ce ko kadan Messi bai kama kafarsa a iya kwallon kafa ba
Asali: Getty Images

Dan wasan da ya zura sama da kwallaye 1000 a rag, kuma ya lashe kofin duniya har sau uku, ya shaidawa kafar watsa labarai ta Brazil, Folha de Sao Paulo, cewa: " Ta ya zaku hada iyawar wanda ya san taka leda kamar cin tuwansa, wada ya iya sa ka, ya iya dukan kwallo da kafar hagu da dama, amma a hada shi da wanda ke iya dukan kwallo da kafar hagu kadai, ya na da bajinta amma ko sa kai bai iya ba?"

"Da aka tashi ma kwatantawa, sai a hada shi da Pele? Lallai mai iya gogayya da Pele sai wanda ya san sirrin dukan kwallo da kafar hagu da dama, kuma ya iya zura kwallo a raga da kai."

Pele ya kara da cewa: "Ni a nawa bangaren, Maradona na daga cikin yan wasan da suka iya taka leda. Idan aka tambaye ni, ko ya zarce Messi? Zan amsa da "Eh, ya zarce Messi ta ko ina.

" Kai hatta ma, [Franz] Beckenbauer, [Johan] Cruyff sun zarce Messi a wajena.”

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Asali: Legit.ng

Online view pixel