Muhimman Bayanai 5 da Ba a Sani Ba a Kan Tarihin Ajiye Makullin Dakin Ka’aba

Muhimman Bayanai 5 da Ba a Sani Ba a Kan Tarihin Ajiye Makullin Dakin Ka’aba

  • Hukumomin kasar Saudiyya sun sanar da rasuwar mai ajiye makullin dakin Ka'aba, Sheikh Saleh Al-Shaibi a yau Asabar
  • Iyalan gidan kabilar Shaiba ne masu ajiye makullin dakin Ka'aba da lura da shi tun zamanin annabta har zuwa wannan lokacin
  • Legit ta tatttaro muku abubuwa masu muhimmanci da ya kamata ku sani a kan ajiye makullin dakin Ka'aba a wannan rahoton

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kasar Saudi Arabia - Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da rasuwar Sheikh Saleh Al-Shaibi a yau Asabar.

Sheikh Saleh Al-Shaibi shi ne wanda yake rike da makullin ɗakin Ka'aba har zuwa rasuwarsa a yau.

Makullin Ka'aba
Wanda ke rike da makullin Ka'aba ya rasu. Hoto: Inside the Haramain
Asali: Facebook

A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan ajiye makullin dakin Ka'aba wanda ya samo asali tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Yana kokarin hana fadan daba, 'Yan tauri sun kashe Shugaban bijilanti a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Masu rike da makullin Ka'aba

Jaridar Alarabiyya News ta wallafa cewa Ƙabilar Bani Shaiba ne ke da ikon ajiye makullin Ka'aba kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya mallaka musu.

Hakan na nuni da cewa ƴan ƙabilar Shaibah ne suke da ikon lura da ayyukan kula da dakin Ka'aba tare da hadin gwiwar hukumomi.

2. Yaushe aka ba su ajiyar makullin?

Tun kafin zuwan addinin Musulunci dama 'yan ƙabilar Shaibah ne ke rike da makullin ɗakin Ka'aba kuma suke masa hidima.

Amma bayan Musulunci ya karbi garin Makka a shekara ta takwas bayan Hijira sai Annabi Muhammad (SAW) ya tabbatar musu da ajiyar makullin har abada.

3. Wa ya rike makullin a zamanin Annabi?

Jaridar Saudi Gazette ta wallafa cewa sahabi Usman bin Ɗalha ne ya rike makullin ɗakin Ka'aba a zamanin Annabi (SAW).

Kara karanta wannan

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, ya nemi ayi sulhu da gwamnati

Annabi (SAW) ya yi umurni da a damƙawa Usman bin Ɗalha makullin bayan an karɓe shi daga wajensa a lokacin da aka samu buɗe garin Makka.

4. Mutane nawa suka rike makullin Ka'aba?

A tsawon tarihi an samu mutane 109 da suka rike makullin Ka'aba wanda na ƙarshen su shi ne Sheikh Saleh Al-Shaibi.

Bayan rasuwar Sheikh Saleh Al-Shaibi a yau ana tsammanin hukumomi a kasar Saudiyya za su naɗa wanda zai cigaba da rike makullin daga iyalan gidan Usman bin Ɗalha (Allah ya kara yarda da shi).

5. Ayyukan mai rike da makullin ka'aba

Masu rike da makullin suna yin dukkan ayyuka da suka shafi kula da dakin Ka'aba ciki har da budewa da kulle dakin idan bukata ta taso.

Har ila yau, su ne masu wanke dakin da ake yi duk ranar 15 ga watan Muharram da sauran ayyukan da suka shafi tsaftace shi da canza masa riga.

Kara karanta wannan

Sarkin da ya fi daɗewa a sarauta a Arewa ya rasu, Bola Tinubu ya tura saƙon ta'aziyya

Dan Najeriya ya yi abin kirki

A wani rahoton, kun ji cewa wani mahajjaci daga jihar Jigawa a Arewacin Najeriya ya nuna kyakkyawan hali yayin da ya tsinci jakar hannu ɗauke da maƙudan kudi a Madinah.

Alhaji Abba Saadu Limawa ya yi cigiya domin bai wa mai jakar kayansa amma ba a ga mai ita ba, don haka ya kai wa hukumar NAHCON.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng