Bafarawa ya shiga dakin Ka'aba (Hotuna)
- Da maraicen jiya ne tsohon gwamna jihar Sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa ya samu karramawa ta mussaman don shiga cikin Daki mai tsarki na Ka'abah bisa amsa gayyatar Babban Limamin Masallacin Harami Sheikh Abdurrahaman Sudais
- A lokacin shigar tasa ya gudanar da sallah nafila raka'a biyu tare da Limamin Massalacin Harami da kuma daukar tsawon mintoci 15 don gudanar da addu'a
Daman dai Majalisar Kolin Musulunci da na Hukumomin Kula da Massalatai Masu Tsarki na Makka da Madinah a lokaci lokaci su kan zabi wasu muhimman mutane daga ko'ina a duniya wadanda suke yiwa Musulunci hidima don basu dama shiga cikin Ka'abah.
A hoton yana saukowa tare da Sheik Saleh Bn Abdullah da Maazeen Sadaam Bn Idrisiyya.
A wani labarin kuma, Ministan watsa labarai, Lai Mohammed yace wannan gwamnati ba ta da wata shiri na boye ko ko a zahiri domin mai da kasa Najeriya kasar musulunci kawai.
Lai mohammed ya fadi hakanne a taron tattaunawa da mutane da akayi a garin Ilori, jihar Kwara.
Lai Mohammed ya ce wannan zancen kanzon kurege ne kawai domin babu irin wannan magana ko mai kama dashi lissafin wannan gwamnati.
Ya kara da cewa ‘yan siyasa ne kawai suke amfani da irin wadannan kalamai domin ingiza mutane da tada zaune tsaye a kasa Najeriya.
Shugabannin addinin Kirista da yawansu sun zargi wannan gwamnati da kokarin mai da kasa Najeriya kasar musulunci.
Asali: Legit.ng