InnalilLahi: An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Jigon APC a Saudiya Yayin Aikin Hajji
- An shiga jimami bayan jigon jam'iyyar APC ta riga mu gidan gaskiya a kasar Saudiyya wajen zuwa aikin hajji
- Marigayiyar mai suna Ramota Bankole ta kasance jajirtacciya a jam'iyyar APC wanda ta rike mukamai da dama
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jami'yyar a jihar, Seye Oladejo ya fitar a yau Alhamis
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Makkah, Saudiyya - Hukumomi sun sanar da rasuwar wata Hajiya kuma jigon jam'iyyar APC a kasar Saudiyya.
Marigayiyar mai suna Ramota Bankole ƴar asalin jihar Lagos ta rasu a kasar yayin da ta je aikin hajji.
Wane mukami Bankole ta rike a APC?
Bankole kafin rasuwarta, ita ce tsohuwar sakatariyar jin dadi ta jam'iyyar APC a jihar Lagos, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren yada labaran jami'yyar, Seye Oladejo shi ya tabbatar da haka a yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024, Vanguard ta tattaro.
"Rasuwarta ta zo mana bazata da kuma jimami, tabbas ta kasance jajirtacciya a jam'iyyar APC."
"Bankole ta kasance mai hidima ga APC wanda ta ke kokarin fadakar da mata kan shiga siyasa, Allah ya mata rahama."
- Seye Oladejo
Shugabar karamar hukuma ta yi jimami
Shugabar karamar hukumar Epe, Surah Animashaun ta yi jimamin rasuwar Bankole a yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024.
Animashaun ta ce marigayiyar lafiyarta kalau ta bar Najeriya zuwa kasa mai tsarki.
Ta tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiyar da karamar hukumar Epe da ma jam'iyyar APC baki daya.
Alhaji daga Plateau ya rasu a Hajji
A wani labarin, kun ji cewa wani Alhaji da ya fito daga jihar Plateau, ya riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki wajen gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024.
Sakataren hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar, Alhaji Hayabu Dauda, ya tabbatar da rasuwar Alhajin mai suna Ismaila Musa, a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.
Alhaji Hayabu Dauda ya bayyana cewa Alhajin ya rasu ne a asibitin ƙwararru na Annur da ke birnin Makkah, inda ya shafe makonni uku yana jinya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng