Sojojin Najeriya Za Su Tafi Maƙwabciyarta Domin Wanzar da Zaman Lafiya, an Jero Dalilai
- Sojojin Najeriya za su cilla kasar Gambia domin taimaka mata wurin wanzar da zaman lafiya da kare lafiyar al'umma
- Dakarun akalla 197 ne aka horas domin sanin aikin da za su je yi a kasar da ke fama da matsalolin tsaro daban-daban
- Wannan matakin na zuwa ne yayin da Najeriya ke cikin tsananin rashin tsaro na garkuwa da mutane da ta'adanci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da shirin taimakawa kasar Gambia da dakaru.
Hukumar ta tabbatar da tura sojoji 197 Gambia domin wanzar da zaman lafiya yayin da suke fama da matsalolin tsaro.
Sojojin Najeriya za su taimakawa Gambia
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban bangaren ayyuka a hukumar, Manjo-janar, Boniface Sinjen ya fitar, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boniface ya hakan yana daga cikin hobbasan shugaban hafsan sojoji, Laftanar-janar, Taoreed Lagbaja domin taimakon kasashen duniya da dakaru.
Ya ce an basu horaswa na musamman da koyar da su dabarun wanzar da zaman lafiya a kasashen duniya.
Jawabin babban jami'in sojan Najeriya
"An shirya ku domin kare lafiyar fararen hula, an koyar da ku hadin kai da shugabanci da kuma kiyaye al'adu domin samun nasara kan abin da kuka je yi."
"Kun samu horaswa domin samar da zaman lafiya a kowace irin al'umma da kuma kiyaye dokar kasa da mutunta ƴancin ɗan Adam."
- Janar Boniface Sinjen
Halin rashin tsaron da Najeriya ke ciki
Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya ta gaza kawo karshen matsalolin tsaro da take fama da su.
Akalla a kowane wayewar gari ana kashe mutane da dama da ba su ji ba, ba su gani ba musamman a Arewacin Najeriya.
Sojoji sun hallaka ƴan IPOB a Abia
A wani labarin, kun ji cewa Rundunar sojoji ta bayyana nasarar da ta samu kan ƴan ta'addan IPOB da ESAN a jihar Abia da kuma kan yan bindiga a jihar Ondo.
A kokarinta na yaki da 'yan ta'adda da wanzar da zaman lafiya, rundunar sojojin Najeriya ta kai farmaki kan ƴan ta'adda a Kudancin kasar.
Hakan na zuwa ne yayin da ƴan ta'addan IPOB ke kara zama barazana ga al'umma da ma hukumomi a yankin Kudu maso Gabas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng