Sojojin Najeriya Sun Ragargaji ’Yan Ta’adda a Jihohin Kudu

Sojojin Najeriya Sun Ragargaji ’Yan Ta’adda a Jihohin Kudu

  • Rundunar sojin Najeriya ta kai tagwayen farmaki kan gungun ƴan ta'adda da suka fitini al'umma a jihohin Abia da Ondo da ke kudancin kasar
  • A jihar Abia, rundunar sojin ta yi nasarar wargaza sansanin yan ta'addan IPOB masu yunkurin kafa kasar Biyafara da kawayensu na ESAN
  • A daya bangaren kuma, rundunar ta hallaka yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Ondo inda ta samu nasarar kwato makamai a wajensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Abia - A kokarinta na yaki da 'yan ta'adda da wanzar da zaman lafiya, rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan ƴan ta'adda a Kudancin kasar.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta dauki matakin gaggawa kan cin zarafin farar hula a Legas

Rundunar sojin ta bayyana nasarar da ta samu kan ƴan ta'addan IPOB da ESAN a jihar Abia da kuma kan yan bindiga a jihar Ondo.

Sojojin Najeriya
Sojojin sun fatattaki 'yan ta'adda a jihohin Abia da Ondo. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne cikin wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook a yau Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun tarwatsa yan IPOB

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa a jiya Laraba ta kai farmaki kan 'yan ta'addan IPOB a karamar hukumar Arochukwu da ke jihar Abia.

Rundunar ta yi nasar fatattakar yan ta'addan IPOB da ESAN daga sansanin da suka kafa a yankin tare da rusa gine-ginen da suka yi.

Ƴan ta'addan suna amfani da sansanin ne wajen ba da horo da renon wasu yan ta'adda domin su rika taimaka musu.

Rundunar sojin ta ce za ta cigaba da kai farmaki kan ƴan ta'addan har sai ta ga bayansu a yankin, kuma za ta rika bayani ga al'umma kan halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kara samun nasara, an harbe 'yan ta'adda a Kaduna

Ondo: Sojoji sun fatattaki yan bindiga

Haka zalika sojojin Najeriya sun kai farmaki kan gungun yan bindiga a karamar hukumar Irele a jihar Ondo.

Sojojin sun fatattaki yan yan bindigar tare da kwato makamai da suka hada da bindiga kirar AK47 daya, bindigogi kirar gida guda biyu da tarin harsashi.

Kaduna: Sojoji sun kashe yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara a ƙoƙarin da suke yi na kawo ƙarshen ƴan bindigan da suka addabi mutane a ƙasar nan.

Sojojin sun samu nasarar hallaka wani gawurtaccen shugaban ƴan bindiga, Buharin Yadi a yayin wani artabu a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng