Miliyoyin Musulmi za su Fara Hajji, Harin Isra'ila ya Hana Mutanen Gaza Zuwa Saudiyya
- Miliyoyin musulmi sun fara hallara domin fara gudanar da aikin hajjin bana, zuwa yanzu musulmi miliyan 1.5 ne su ka taru, ana sa ran yawansu zai kai miliyan biyu zuwa anjima
- A musulmin da su ka amsa kiran Allah SWT babu al'umar Gaza, wanda harin da Isra'ila take kai wa kan mutane yankin da rufe iyakar Rafah da ke daf da Masar ya hana su zuwa Saudiyya
- Musulmi da dama sun fara mika kukansu da Allah SWT yayin da su ka fara dawafi cikin tsananin zafi kan kisan kiyashin da sojojin Isra'ila ke yi wa mutanen Gaza
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Saudi Arabia- Miliyoyin musulmi ne su ka amsa kiran Allah yayin da su ka hallara a tantunansu a cikin shirinsu na fara aikin hajjin bana a hukumance.
Akalla musulmi sama da miliyan 1.5 ne suka hallara a ciki da kewayen Makkah, kuma ana sa ran adadin zai karu idan musulmin da ke zaune a kasar Saudiyya su ka hadu da sauran musulmin domin ziyarar dakin ka’aba.
Arab New ta wallafa cewa ana sa ran adadin musulmin zai haura miliyan biyu duk da cewa harin da Isra’ila ke kaiwa mutanen Gaza ya hana musulmin yankin ziyartar kasa mai tsarki domin sauke farali a bana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babu musulmin Gaza a aikin hajji
Luguden wuta da kisan kiyashin da kasar Isra’ila ke yiwa al’umar Gaza yah ana muslmin yankin bin sahun sauran musulmi wajen sauke farali a kasa mai tsarki.
Yayin da musulmi su ka fara dawafi a yau Juma’a, da yawa daga cikin musulmi sun a mika kukansu ga Allah kan yadda Isra’ila ke kashe mutanen Gaza, kamar yadda Aljazeera News ta wallafa.
“Yan uwanmu na mutuwa, kuma muna ganin hakan da idanunmu,”
-Zahra Benizahra ‘yar shekaru 75 daga Morocco.
Falasdinawa daga yankin Gaza sun gaza zuwa Saudiyya bayan rufe iyakar Rafah dab da iyakar kasar Masar da dakarun Isra’ila su ka yi.
Shugabannin jihar Neja sun tafi aikin hajjin
A wani labarin kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammaed Umaru Bago, mataimakinsa, Yakubu Garba da Kakakin majalisar dokokin jihar Barista Abdulmalik Sarkin-Daji sun tafi aikin hajji.
Tuni jam'iyyar PDP a jihar ta yi Allah wadai da matakin da dukkanin shugabannin su ka dauka na barin al'umarsu, yayin da wasu al'umar jihar ke ganin an yi watsi da lamuransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng