Tinubu da Sauran Shugabannin Kasashen Duniya 5 da Suka Taɓa Faduwa a Matakala
Ƴan Najeriya suna ta maganganu bayan faduwar Bola Tinubu yayin taron dimukradiyya a Abuja a yau Laraba 12 ga watan Yuni.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Bola Tinubu ya yi tuntube ne da matakalar hawa mota domin duba faretin da ake gudanarwa a filin taro na Eagle Square a Abuja.
Sai dai bayan Bola Tinubu, akwai wasu shugabannin kasashen duniya da suka taba faduwa yayin hawa jirgi ko abin hawa, cewar Punch.
Legit Hausa ta jero muku shugabannin kasashen da suka gamu da tsautsayin a kokarin sauka ko hawa matakala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Amurka, Gerald Ford - 1975
Shugaban kasar Amurka a 1975, Gerald Ford ya yi tuntube da matakalar jirgi yayin ziyara a kasar Austria.
2. Cuba, Fidel Castro - 2004
Fidel Castro ya fado daga matakala inda ya karya guiwarsa da hannunsa yayin lamarin a shekarar 2004.
3. Zimbabwe, Robert Mugabe - 2015
A shekarar 2015, Robert Mugabe mai shekaru 90 ya fadi daga matakalar jirgi bayan jawabi ga magoya bayansa a birnin Harare.
4. Amurka, Barack Obama - 2015
Barrack Obama ya yi tuntube da matakalar jirgi wanda ya kusa faduwa bayan dawowa birnin Washington DC a 2015.
5. Russia, Vladmir Putin - 2019
Shugaban kasar Russia, Vladmir Putin ya kife lokacin da ya ke buga wasan Ice Hockey kafin daga bisani aka tallafa masa.
6. Amurka, Joe Biden - 2021
Shugaba Joe Bayan ya sha da kyar bayan tuntube da matakalar jirgi a 2021 yayin kai ziyara Atlanta.
Shugabannin da suka fadi kafi Tinubu
Sauran manyan mutane da suka zame sun hada da Sakatariyar Gwamnatin Amurka a 2011, Hillary Clinton sai Sanata Tommy Tuberville a 2023.
Sai kuma mataimakin shugaban kasar Amurka a 2020, Mike Pence wanda ya fadi yayin saukowa daga matakalar jirgin sama.
Atiku ya jajantawa Tinubu kan zamewa
Kun ji cewa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya jajantawa Bola Tinubu kan zamewa da ya yi a birnin Abuja.
Atiku ya nuna damuwa kan yadda shugaban ya gamu da tsautsayi inda ya yi masa fatan alheri da kuma kasancewa cikin lafiya.
Hakan ya biyo bayan zamewa da shugaban ya yi a matakalar hawa mota domin duba masu fareti a filin 'Eagle Square' da ke Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng