Duk da Dokar Hana Masu Ciki Aikin Hajji, Hajiyar Najeriya Ta Haifi Jaririn Farko a Makkah

Duk da Dokar Hana Masu Ciki Aikin Hajji, Hajiyar Najeriya Ta Haifi Jaririn Farko a Makkah

  • Duk da tsauraran dokoki da ke hana masu juna biyu zuwa aikin hajji, wata Hajiya daga jihar Borno ta haifi jariri a Saudiyya
  • Hukumomin kasar Saudiyya sun tabbatar da cewa matar ta haifi namijin jariri wanda aka sanyawa suna Muhammad
  • Jami'an lafiya na Hukuma NAHCON sun tabbatar da samun rahoton inda suka ce ta kaucewa binciken da ake yi a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Makkah, Saudiyya - Wata Hajiya daga jihar Borno ta samu karuwa inda ta haifi yaro namiji a kasar Saudiyya yayin aikin hajji.

Matar mai shekaru 30 ta haihu ne bayan an kwantar da ita a asibitn Makkah da ke kasar bayan fara jin nakuda.

Kara karanta wannan

Hajj: Najeriya ta kammala jigilar alhazanta zuwa kasa mai tsarki

Hajiya daga Najeriya ta haihu yayin aikin hajji a Saudiyya
Wata Hajiya daga jihar Borno ta haihu a kasar Saudiyya. Hoto: Saudi Gazette.
Asali: Facebook

Saudiyya: Mata ta haihu yayin aikin hajji

Saudi Gazette ta tabbatar da cewa an kwantar da matar ne bayan ta cika makwanni 31 da juna biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu ba da agajin gaggawa sun bata kulawa na musamman yayin da aka kai ta dakin haihuwa inda ta yi nasarar haifar yaro namiji.

Yayin da matar ke ci gaba da samun kulawa, an radawa jaririn suna Muhammad inda shi ma ake ba shi kulawa na musamnan.

Wannan shi ne haihuwa na farko da aka samu a hajji ta bana bayan rasuwar mahajjata da dama a kasar.

Hajji: NAHCON ta magantu kan lamarin

Jagoran jami'an lafiya na hukumar NAHCON, Dakta Abubakar Isma'il ya tabbatar da lamarin inda ya ce matar ta fito daga jihar Borno.

Daktan ya ce sun samu rahoton daga jami'an lafiya daga sansanin jihar Borno inda ya ce matar ta gujewa binciken lafiya da ake yi tun daga Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamanti ta fadi yadda za ta kwato bashin da ta rabawa mutane a lokacin Corona

Wannan na zuwa ne duk da dokar NAHCON kan hana masu juna biyu zuwa aikin hajji amma ana ci gaba da samun haihuwa da dama a lokutan aikin hajji.

Hukumar ta tabbatar da samun haihuwar jarirai 75 a aikin hajjin bara da aka gudanar bayan kaucewa bincike mai tsauri da ake yi.

Wata hajiya ta rasu a Saudiyya

Kun ji cewa wata hajiya daga jihar Kebbi ta riga mu gidan gaskiya a Saudiyya yayin gudanar da aikin hajjin bana.

Rahotanni sun tabbatar da cewa matar mai suna Tawalkatu Busare Alako ta rasu ne a kasar bayan ta gamu da rashin lafiya a birnin Makkah.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel