InnalilLahi: Wata Hajiya Daga Najeriya Ta Hallaka Kanta a Madina, Saudiyya Ta Yi Martani
- Yayin da ake yawan samun mace-mace a Saudiyya, wata Hajiya daga jihar Kwara Najeriya ta riga mu gidan gaskiya
- Hukumomin Saudiyya sun tabbatar da cewa matar mai suna Hajiya Hawawu ta rasu ne bayan yin ajalin kanta
- Wannan na zuwa ne bayan rasuwar wani Alhaji daga jihar mai suna Saliu Mohammed bayan gamuwa da rashin kafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Madina, Saudiyya - Ana zargin wata Hajiya mai suna Hawawu ta hallaka kanta a birnin Madina da ke kasar Saudiyya.
Hajiyar ta fito ne daga jihar Kwara inda hukumomin Saudiyya suka tabbatar da haka bayan gudanar da bincike.
Hajji: Hajiya ta rasu a Saudiyya
Hukumomin sun sanar da hukumar alhazai ta jihar Kwara yadda al'amarin ya faru a Madina bayan samun gawar matar, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren hukumar, Abdulsalam AbdulKabir ya sanyawa hannu, Leadership ta tattaro.
Sanarwar ta ce hukumomin Saudiyya sun gudanar da bincike inda suka tabbatarvda cewa ta yi ajalin kanta ne a saman dakinta da ke Madina.
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar wani mahajjaci daga jihar Kwara mai suna Saliu Mohammed wanda ya rasu bayan faduwa rashin lafiya.
Kwara: Hukumar alhazai ta yi martani
Hukumar alhazai ta jihar Kwara ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu a kasar Saudiyya daga jihar.
"Saliu Muhammad ya rasu bayan an kai shi asibiti a birnin Madina yayin da Hajiya Hawawu Mohammed hukumomi suka tabbatar ta yi ajalin kanta."
"Hukumar alhazan ta nuna takaici kan rashin da aka tafka guda biyu a jihar amma ta mika duka lamarinta ga Allah."
- Abdulsalam AbdulKabir
Hajiya daga Niger ta rasu a Saudiyya
Kun ji cewa wata Hajiya daga jihar Niger mai suna Ramatu Abubakar ta riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki a Saudiyya.
Hajiyar mai shekara 45 a duniya ta rasu ne a birnin Madinah na ƙasar Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin bana.
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar wasu 'yan Najeriya daga jihohi da suka haɗa da Kebbi da kuma Lagos da jihar Kwara.
Asali: Legit.ng