Kasar Saudiyya Ta Kama Masu Damfarar Mutane Domin Sama Musu Izinin Aikin Hajji

Kasar Saudiyya Ta Kama Masu Damfarar Mutane Domin Sama Musu Izinin Aikin Hajji

  • Biyo bayan matakan tsaurara tsaro da kasar Saudiyya ta dauka a kan aikin Hajji, ta kama yan damfara guda hudu
  • Jami'an tsaron Saudi na musamman masu kula da ayyukan Hajji ne suka kama mutanen kamar yadda kasar ta sanar
  • Hukumomi sun bayyana irin abubuwan da aka kama yan damfarar dauke da su da kuma ƙasashen da suka fito

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kasar Saudi Arabia - A yau Alhamis, 6 ga watan Yuni kasar Saudiyya ta sanar da kama yan damfara guda hudu.

Mutanen wanda dukkan su maza ne ana zarginsu da damfarar al'ummar Musulmi a kan gudanar da aikin Hajjin wannar shekarar.

Kara karanta wannan

Kasar Saudiyya ta dauki tsauraran matakai kan masu zuwa hajji ta barauniyar hanya

Yan damafara a Makka
An kama masu jigilar Hajji na bogi a Makka. Hoto: Inside the Haramain
Asali: Facebook

Shafin sada zamunta mallakin kasar Saudiyya mai suna Inside the Haramain ne ya wallafa labarin a kafar Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Laifin da yan damfarar suka aikata

Shafin ya tabbatar da cewa mutanen suna damfarar al'ummar Musulmi ne ta yanar gizo da sunan za su samar musu da iznin zuwa Hajji.

Dama dai kasar Saudiyya ta dauki tsauraran matakai domin dakile masu zuwa Hajji ta barauniyar hanya.

Daga wace kasa mutanen suka fito?

Rahotanni sun yi nuni da cewa mutanen su hudu ne kuma biyu daga cikin su 'yan asalin ƙasar Saudiyya ne.

Sai kuma sauran mutane biyun sun fito daga kasar Pakistan inda suka hada kai suna damfarar al'ummar Musulmi.

Kayan da aka kama wajen yan damfarar

Hukumomin Saudiyya sun tabbatar da kama wasu daga cikin kayan da mutanen suke amfani da su wajen gudanar da ayyukan damfara.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta hana Alkalai zaman kotu saboda yajin aiki a Abuja

Daga cikin abubuwan da aka kama akwai layukan waya da dama, wayoyin hannu, na'ura mai ƙwaƙwalwa da dama da kuma makudan kudi.

NDLEA ta kama maniyyata a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar yaƙi da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta samu nasarar kama maniyyata aikin Hajjin bana dauke da hodar Iblis.

Rahotanni sun nuna cewa jami'an hukumar sun kai samame otel din da alhazan hudu suke zaune inda aka kama su suna shirin haɗiye ledoji 200 na hodar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel