An Cafke Hatsabibin Ɗan Bindiga Baleri? Bello Turji Ya Fadi Komai a Wani Faifan Bidiyo
- Bayan dakarun kasar Nijar sun tabbatar da kama Baleri, Bello Turji ya fito ya kalubalance su a cikin wani faifan bidiyo
- Hatsabibin ɗan bindiga, Turji ya ƙaryata rade-radin kamawa ko hallaka Baleri inda ya ce abin kunya ne yadda sojoji ke karya
- Turji ya daga hannun Baleri a cikin faifan bidiyon inda ya ce babu kamshin gaskiya kan wannan labarin kanzon kurege
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Nijar - Hatsabibin ɗan ta'adda, Bello Turji ya fitar da sabon faifan bidiyo inda ya ke kalubalantar sojojin jamhuriyar Nijar.
Turji ya ƙaryata labarin cewa dakarun sun cafke Baleri inda ya nuna shi a cikin faifan bidiyon.
Bello Turji ya ƙaryata cafke Baleri
A cikin faifan bidiyon da Zagazola Makama ya wallafa an gano mayaka zagaye da Turji da muggan makamai inda ya ke jan kunnen hukumomi a Nijar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya shawarci shugaban kasar da ya bar kashe talakawa da cutar da su kada talakawa su dauki makamai kamar yadda suma suka yi a Najeriya.
"A haka aka fara a Najeriya, a kashe talakawa kuma a ce an kashe ƴan bindiga wanda shi ya saka muka dauki makamai."
"Kai gwamnan Maradi da ka ce ka kama Baleri to ga shi nan da kuma kwamandojin Bello Turji da dama a nan."
"Sun ce an kama Baleri an kashe Baleri to gashi nan bari in nuna muku shi a kusa da ni da wasu mayaka da dama a nan."
- Bello Turji
Turji ya kalubalanci sojoji kan Baleri
Turji ya ce hukumomi sun ji kunya kan yadda suke yada karya sun cafke mutanensa guda 60 inda ya ce su ƴan bindiga ba su karewa ne a duniya.
Ƴan bindiga sun sace matar sarki
A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai wani farmaki jihar Kaduna a daren jiya Laraba 5 ga watan Yuni.
Maharan sun yi awon gaba da matar sarkin Ninzo da ke karamar hukumar Sanga a jihar yayin harin da da suka kai.
Rundunar 'yan sanda a jihar, ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce ta baza jami'an tsaro neman matar a cikin dazuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng