Jirgin Sama Dauke da Shugaban Kasar Iran Ya Samu Matsala, Ya Yi Muguwar Saukar Gaggawa

Jirgin Sama Dauke da Shugaban Kasar Iran Ya Samu Matsala, Ya Yi Muguwar Saukar Gaggawa

  • Shugaban kasar Iran ya yi hadari a jirgin sama da safiyar ranar Lahadi 19 ga watan Mayun 2024, inji rahotanni
  • An bayyana dalilin da yasa shugaban na Iran ya tafi ziyara Azabaijan, inda ya gana da shugaban kasar a ranar
  • Iran kasa ce mai yawan abokan gaba, musannan daga yammacin duniya da kuma Turawan da ke da alaka da kasashen Amurka

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Kasar Iran - Rahotanni daga kasar Iran sun bayyana cewa, wani jirgi mai saukar ungulu ya samu tsaiko dauke da shugaban kasar Ebrahim Raisi ya samu tsaiko.

Kafar labaran kasar ta ce, lamarin ya auku ne a lokacin da shugaba Raisi ke kan hanyarsa ta zuwa yankin lardin Azabaijan ta Gabashin Iran.

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

Jirgin ya yi saukar gaggawa ne a yankin Jolfa da ke iyaka da Azabaijan mai tazarar kilomita 600 daga Arewa maso Yammacin Tehran, babban birnin Iran, rahoton Alsharq Awasat.

Jirgin shugaban Iran ya fadi a kusa da kasar
Jirgin shugaban Iran ya yi mummunar sauka a kasar | Hoto: Ali Hamed Haghdoust/IRNA via AP
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kadai ne hadarin ya rutsa dashi?

A tare da shugaban, akwai ministan harkokin wajen kasar, Hossein Amirabdullahian, gwamnan Gabashin Iran na lardin Azabaijan da sauran jiga-jigan gwamnati.

Tuni dai jami’an kwana-kwana suka taru don tabbatar da ba a samu asarar rai ba a daidai da jirgin ya yi saukar gaggawa bayan lalacewar injinsa.

An kuma ruwaito cewa, an samu aukuwar ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma iska mai karfi a lokacin da lamarin ya faru, AlJazeera ta ruwaito.

Dalilin zuwan shugaban Iran Azabaijan

Shugaban ya tafi yanin Azabaijan ne da sanyin safiyar Lahadi don kaddamar da wata madatsar ruwa tare da shugaban kasar, Ilham Aliyev.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: EFCC za ta binciki 'dan majalisa kan daukan nauyin ta'addanci

Madatsar ruwan irinta ta uku kenan da gwamnati ta gina a yankin kogin Aras da ke tsakanin kasashen biyu.

Iran dai kasa ce da ke da yawan Musulmai, kuma babbar abokiyar gaban kasashe ne da dama a yammacin duniya.

Rikicin Iran da Isra'ila

A wani labarin, takaddamar da ta barke tsakanin kasar Isra'ila da Iran na cigaba da jan hankulan al'ummar duniya.

Rikicin ya sa mutane da dama ciki har da shugabannin duniya suke hasashen cewa idan yakin ya barke tsakanin kasashen biyu zai iya kawo babban tashin hankali a gabas ta tsakiya.

Wasu masu sharhi suna ganin illar rikicin ba za ta tsaya a gabas ta tsakiya bane kawai, za ta iya shafan duniya baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.