Sojoji Sun Gayyaci, Yarima Harry da Meghan, Za Su Kawo Ziyara Najeriya
- Yarima Harry da matarsa sarauniya Meghan za su kawo ziyara Tarayyar Najeriya gobe Juma'ah, 10 ga watan Mayu
- Ziyarar ta samo asali ne daga gayyata da rundunar tsaron Najeriya ta musu kuma za ta kai tsawon kwanaki uku
- An bayyana wurare na musamman da za su ziyarta da fitattun mutanen da za su gana dasu a lokacin ziyarar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Yarima Harry Charles na kasar Birtaniya da matarsa Meghan Markle za su kawo ziyara Najeriya a gobe Juma'ah, 10 ga watan Mayu.
Rahotanni sun nuna cewa za su kawo ziyarar ne a karkashin gayyatar da hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya musu.
Kwana nawa Harry & Meghan za suyi?
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa za su shafe kwanaki uku ne a Najeriya suna ziyarar wurare mabanbanta daga ranar 10 zuwa 13 ga watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za su iso Najeriya ne a gobe Juma'ah da misalin karfe 12:00 na rana kuma za su fara yada zango a makarantar da suke tallafawa ta Wuse Light Academy.
Wuraren da Harry, Meghan za su ziyarta
Daga cikin wurare na musamman da za su ziyarta akwai Asibitin sojoji da suka ji raunuka dake jihar Kaduna.
Ana sa ran za su gana da sojojin da ke asibitin dama iyalansu a lokacin ziyarar domin karfafa musu gwiwa.
Bayan ziyartar sojojin, Yarima Harry da sarauniya Megham za su gana da gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani.
Daga nan ne za su tafi zuwa Lagos domin ganawa da gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu.
Bayan haka za su kai ziyara wajen kwallon kwando na makarantar da suke tallafawa a jihar ta Lagos.
Bayan sun yi liyafa a Lagos ranar Lahadi za su dawo Abuja su fara shirye-shiryen komawa gida Birtaniya.
An nada sarki Charles gadon sarauta
A wani rahoton, kun ji cewa a ranar Asabar 6 ga watan Mayu ne Burtaniya ta nada sarki Charles II watanni takwas bayan hawansa sarauta biyo bayan mutuwar mahaifiyarsa.
Sarki Charles ya yi rantsuwa da Allah cewa, zai yi mulkinsa da adalci da tausayi, kuma zai yi aiki da daidai da mazhabobin addinin kirista na cocunan Anglican da kuma Presbyterian.
Asali: Legit.ng