Ababe 4 da ya kamata ku sani game da Sabuwar Amaryar Masarautar Ingila

A yayin da a yau ne aka daura auran Yarima Harry da kuma sahibar sa Gimbiya Meghan Markle, Legit.ng ta kawo muku wasu ababe 4 da ya kamata ku sani game da wannan sabuwar amarya.

Ita dai Rachael Meghan Markle haifaffiyar kasar Amurka ce domin kuwa ba ta dangantaka ta kusa ko ta nesa da kasar Ingila ballantana ta kai ga Masarautar ta.

An haife ta a ranar 4 ga watan Agusta na 1981 wanda yake nuna cewar ta dara sabon angon nata da shekaru 3 a sakamakon an haifeshi ne a ranar 15 ga watan Satumba na 1984.

Fitacciyar jarumar tana kuma da nasaba da bakar fata ta nahiyyar Afirka da ta samo tushe ta silar mahaifiyar ta da ta kasance ruwa biyu. Ta kuma yi karatun ta a Jami'ar Northwestern University dake kasar Amurka fannin Nazarin Theater and International Studies.

A baya dai Gimbiya Meghan ta auri wani jarumi, Trevor Engelson, a shekarar 2004, inda suka rabu a watan Agusta na 2013.

An gudanar da wannan biki ne a babbar Cocin St George Chapel inda kuma daga nan suka dugunzuma ta hanyar Windsor zuwa wajen liyafa ta tande-tande da makwalashe a harbar taro ta Frogmore House da ta samu halartuwa ta baki 600.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya za ta fadada Shirin N-Power - Osinbajo

Rahotanni sun bayyana cewa, da yawan shahararrun masu sana'ar nishadantarwa sun halarci wannan biki da suka hadar da 'yan kwallo, mawaka da kuma masu sana'ar shirya fina-finan a nahiyyar Turai.

Legit.ng ta fahimci cewa, an gudanar da wannan biki ne da misalin karfe 12.30 na tsakar ranar yau ta Asabar, inda hasashen maruwaita ya bayyana cewa an gudanar da bikin ne a wannan lokaci sakamakon cin karo yake da wasan karshe na tantance zakaran FA Cup na kasar Ingila da za a kara da kugiyar kwallon kafa ta Chelsea da kuma Manchester United da yammacin ranar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel