Bambarakwai: Jerin Kasashe 5 da Mata Ke Biyan Mazaje Sadakin Aure
A tsarin shari'ar Musulunci ango ya ke ba amarya kudin sadaki yayin da ya ke neman aure wanda ke tabbatar da mutuntata a matsayin 'ya mace.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Haka nan a Arewacin Najeriya wanda suke mafi yawan Musulmai sun bin tsarin addinin Musulunci ne wurin gudanar da bikin aure.
Bambance-bambance a yanayin biyan sadakin aure
Sai dai a wasu al'adu da kasashe, mata ke ba maza sadaki yayin shirye-shiryen gudanar da biki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan tsari na wadnnan kasashe ya sabawa al'adun mutane da dama da maza ke ba mata ko iyalansu sadaki a matsayin kudin aure, cewar rahoton Tribune.
Legit Hausa ta jero muku kasashen da mata ke ba maza sadaki.
1. Kamaru
Kabilun Bamileke da Beti suma suna daga cikin yarukan da mata ke ba maza sadaki da suka da kudi dabbobi da sauransu.
Yanayin sadakin da za a bayar ya danganta ne da martabarsu a al'umma ko kuma darajar amarya.
2. Indiya
Ƙasar Indiya na daya daga cikin kasashen da ke dabbaka wannan al'ada tun tali-tali wanda ya zama jiki fa al'umma da dama.
Idan mace ta tashi yin aure, gidan amare ne ke ba gidan maza kudi ko kyaututtuka a matsayin sakaki.
3. Kenya
A wasu yankuna da ke Yammacin Kenya kamar Luhya, ana samun bambanci kan yadda ake biyan sadaki.
A yayin bikin aure, amarya za ta dauki sadaki da hannunta inda za ta ba mahaifin ango da za ta aura.
4. Rwanda
A al'adun mutanen Gusaba, mata suna neman izinin maza a aure tare da ba su sadaki saboda nuna godiya da mutuntawa.
Daga cikin kayan akwai dabbobi da kayan sakawa da kuma kayan amfanin gida wanda ke nuna gidansu amarya sun shirya aure.
5. Mauritania
A wasu al'adun kasar Mauritania da ake kira 'Mahr' mata na biyan sadaki yayin bikin aure domin mutunta gidan mazaje.
Daga cikin kayan da ake bayarwa akwai kudi da gwal wanda ke nuna darajar amarya wanda miji ke gane muhimmancin mace.
Tattaunawar Legit Hausa ta malamin Musulunci
Legit Hausa ta ji ta bakin malamin Musulunci kuma lakcara a Jami'ar Tarayya ta Kashere da ke Gombe.
Malam Muhammad Umar ya ce sadaki tsari ne na Musulunci wanda ya wajabtawa maza su ba mata
"Sadaki dai wani tsari ne na shari'a da Allah Ya daurawa maza su ba mata don nuna karfinsu da shugabancinsu a kan mata."
"Shi dai sadaki wajibi ne a Musulunci kuma hakki ne da ake ba mace, kuma ba sharadi ba ne sai an ambace shi ko an ba da shi wajen daurin aure."
"Kuma ba ya nuna cewa ka ba da shi ne a matsayin ka sayi mace ko don jin dadi da ita wurin kwanciya, tunda in wannan ne kowa yana jin dadi da dan uwansa a wajen kwanciya."
- Muhammad Umar
Kasashen da ke amfani da Yaren Hausa
A wani labarin, an ji Hausawa suna da tarihi na musamman a duniya wanda mafi yawansu ke rayuwa a Arewacin Najeriya.
Akwai wasu ƙasashen Nahiyar Afirka da ke amfani da harshen Hausa bayan kasar Najeriya musamman a Arewacin kasar
Daga cikin kasashen akwai Chadi da Kamaru da Nijar da sauransu wanda suka kafa tarihi a kasashen sa suke zaune.
Asali: Legit.ng