Falasdin: Amurka ta Dakatar da Taimakawa Babbar Kawarta Isra'ila da Bama Bamai
- Kasar Amurka a karon farko ta yi jan kafa wajen taimakawa babbar kawarta, Isra’ila a harin da take kai wa kan Falasdinawa
- Wani jami’in Amurka ya bayyana cewa an dakatar da kai wasu manyan bama-bamai Isra’ila don fargabar kai hare-hare Rafah
- Kimanin mutane miliyan daya ne su ka nemi mafaka a yankin Rafah bayan harin sojojin Isra’ila ya tarwatsasu daga gidajensu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
USA- Biyo bayan kin bin umarni da shawarwari da kasar Isra’ila ta yi na ci gaba da kai hare-hare zirin Gaza, yanzu haka babbar kawarta Amurka, ta dakatar da sayar mata bama-bamai.
Wannan shi ne karon farko da shugaban kasar Amurka, Joe Biden da ya rantse ba zai daina taimakawa Isra’ila wajen kaiwa Falasdinawa hari ba ya dan yi jan kafa.

Source: Getty Images
Kisan Falasdinawa ya hana Amurka kai bam
Channels Television ta tattaro cewa wani jami’i a gwamnatin Amurka ya ce an dauki matakin ne saboda fargabar Isra’ilan za ta kaiwa Falasdinawan da suka yi gudun hijira zuwa yankin Rafah hari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin na zuwa ne bayan rahotanni sun ce rundunar sojin Isra’ila ta kwace iko da mashigar Rafah ta bangaren Gaza.
Dalilin Amurka na dakatar da taimakawa Israila
Wani babban jami’i a gwamnatin Amurka da Joe Biden ke jagoranta, ya ce sun dakatar da kai bama-bamai Isra’ila ne saboda fargabar za a yi amfani da shi kan farar hula a Rafah.
Jami'in ya bayyana cewa tun a makon da ya gabata ne Amurka ta dakatar da kai wasu manyan bama-bamai kamar yadda aka tsara za a kai tun da fari.
A rahoton da DW ta wallafa, sama da Falasdinawa Miliyan daya ne ke neman mafaka a yankin Rafah tun bayan da Isra’ila ta fara kai hare-hare Gaza a bara.
Jami’in ya ce suna ta tattaunawa kan yadda za a bullowa lamarin bama-baman.
Turkiyya ta yanke alaka da Isra’ila
A baya kun ji cewa shugaban kasar Turkiyya, Recep Erdogan ya datse alakar kasuwanci tsakanin kasarsa da Isra’ila biyo bayan hare-haren da take ci gaba da kaiwa kan fararen hula a Gaza.
Alakar da Turkutta ta dakatar ya shafi dukkanin bangarorin cinikayya kamar yadda ma’aikatar kasuwancin kasar ta bayyana.
Asali: Legit.ng

