Dama Ta Samu: Yadda ’Yan Najeriya Za Su Iya Yin Karatu Kyauta a Kasar Birtaniya

Dama Ta Samu: Yadda ’Yan Najeriya Za Su Iya Yin Karatu Kyauta a Kasar Birtaniya

  • Wata jami'ar kasar waje ta goron gayyatar neman tallafin karatu ga daliban Najeriya da ke son yin karatu a kasashen waje
  • Jami'ar da ke a kasar Burtaniya ta bayyana cewa za ta dauki nauyin karatun duk wanda ya yi nasarar samun tallafin
  • Sai dai jami'ar za ta tallafawa daliban da ke son yin digiri na biyu ne kawai waɗanda ke da sakamako mai kyau a digiri na farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jami'ar East Anglia da ke Burtaniya ta bayyana cewa ta bude kofar ba da tallafin karatu ga 'yan Najeriya da ke sha'awar yin karatu a kasashen waje.

Haka zalika mazauna wasu kasashen da ba Najeriya ba za su iya neman tallafin karatun, kuma za a cike bukatar neman tallafin ne ta intanet.

Kara karanta wannan

Jami'ar Najeriya ta dauki mataki kan malamin da aka kama yana lalata da daliba

Jami'ar East Anglia da ke Burtaniya za ta bude ba 'yan Najeriya tallafin karatu
Jami'ar Burtaniya burtaniya za ta ba 'yan Najeriya tallafin karatu na N44m. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tallafin N44.3m ga daliban Najeriya

Kamar yadda bayanai a shafin yanar gizon na jami'ar suka nuna, duk wanda ya yi nasarar samun tallafin, zai karbi Naira miliyan 5.1 a matsayin kudin sufuri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa jimillar kudin tallafin karatun ya kai Naira miliyan 44.3, wanda za a baiwa daliban da suka yi nasara.

Tallafin karatun mai taken 'David Sainsbury Scholarships', ya ta'allaka ne kan daliban da ke sha'awar yin karatu a fannin Lafiyar Tsirrai.'

Bayanai a kan shafin yanar gizon UEA sun nuna cewa:

"Ma damar kun cika ka'idojin da ake bukata, kai tsaye za ku shiga jerin wadanda za a iya ba tallafin karatun, za a ba wadanda suka cancanta ne kawai."

Abubuwan da dalibai ke bukata

  • Nuna shaidar kammala digirin farko a fannin ilimin lafiyar tsirrai.
  • Dalibi ya fita da darajar karatun digiri da matakin CGPA 4.1 ko sama da haka.
  • Shaidar samun karramawa daga wasu ayyuka da dalibi ya yi su kan tsirrai.
  • Kwarewa da nuna tsantsar sha'awar yin bincike mai zurfi kan rayuwar tsirrai.
  • Ilimi kan kimiyyar bayanai, musamman a bangaren sanayyar halittu.

Kara karanta wannan

Farin ciki a jihar Arewa yayin da farashin shinkafa ya karye daga N60, 000

Abuja: An rufe makarantar Lead British

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa mahukunta sun rufe wata makarantar kudi ta Burtaniya da ke Abuja bayan bullar bidiyo da ya nuna ana cin zarafin wata daliba.

Shugabannin gudanarwar makarantar sun dakatar da karatu har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan lamarin wanda ya jawo cece-kuce a yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.