Falasdinu da Isra’ila: Hana Musulmar Daliba Jawabin Bankwana Ya Tayar da Kura a Amurka
- Jami'ar Southern California da ke ƙasar Amurka ta dauki matakin hana wata daliba Musulma gabatar da bayanin bankwana saboda rikicin Falasɗinu da Isra'ila
- Jami'ar ta ce ta dauki matakin ne biyo bayan barazana da ta samu daga sauran daliban makarantar a kan cewa dalibar ta na goyon bayan Falasɗinawa
- Dalibar mai suna Asna Tabassum ta bayyana yadda ta ji bayan jami'ar da dauki matakin kasancewar ta saka rai domin yin jawabin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Jami'ar Southern California da ke kasar Amurka ta dau matakin hana wata daliba Musulma bayanin bankwana saboda rikicin Falasdinu da Isra'ila.
Dalibar mai suna Asna Tabassum an zabe ta ne cikin daliban da za su yi jawabi yayin bikin kammala karatunsu a jami'ar.
Ana sa ran duk wanda aka zaba ya yi jawabin zai gabatar da shi ne a gaban mutane sama da 65,000
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ko meyasa aka hana Tabassum jawabi?
Hanata jawabin ya biyo bayan barazana da jami'ar ta samu ne daga sauran daliban makarantar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa daliban makarantar sun ce basu yarda a ba ta damar yin bayanin ba ne saboda tana goyon bayan Falasɗinawa.
Saboda haka jami'ar ta bada sanarwa ranar Litinin da ta gabata cewa za a yi taron ba tare da bawa Tabassum damar yin jawabin ba.
Wasu rahotanni sun nuna cewa jami'ar ta dauki matakin ne saboda dalilai na tsaro, cewar ABC News
Martanin da Tabassum ta yi
Dalibar ta yi martani a kan lamarin musamman kasancewar ana zaban dalibi ya yi jawabin ne saboda kokarin da ya nuna.
Ta yi martani ta na mai cewa an dauki matakin ne saboda nuna kiyayya da kuma nufin hana ta fadin albarkacin bakinta.
Ta kara da cewa, da jami'ar ta bata dama, ranar za ta kasance ranar farin ciki gareta, da malamanta da iyayenta. Amma dai masu kin Falasɗinawa sun yi nasara a kan jami'ar.
Dalibar ta cigaba da cewa ta yi matuƙar mamaki da jami'ar ta yi aiki da maganganun masu nuna tsana da kiyayya.
Martanin kungiyar Musulmai
Daraktan kungiyar Musulmai ta Los Angeles, Hussam Ayloush ya yi Allah wadai da matakin da jami'ar ta dauka
Ya kuma yi kira ga jami'ar da ta gaugauta canja matakin domin bawa kowane dalibi dama ba tare da nuna bambanci ba.
An tilastawa Musulmi aske gemu a Amurka
A wani rahoton kuma kun ji cewa, an tilastawa wani kamfanin Amurka mai suna Blackwell biyan tarar dala dubu 70 bayan da ya tilasta wani ma'aikaci Musulmi aske gemunsa
Hukumar tabbatar da daidaito a wajen daukar aiki ta Amurka EEOC ce ta shigar da karar bayan gaza sasanta mutumin da kamfanin.
Asali: Legit.ng