Ba da Mu Ba Saudiyya ta Musanta Tallafawa Isra'ila a Harin Martanin da Iran ta kai Kwanan Nan
- Wata majiya ta ce kasar Saudiyya ba ta bai wa Isra'ila gudunmawa wajen kakkabo jirage marasa matuka da Iran ta harba mata ba
- Iran ta harba jirage masu linzami da marasa matuka cikin Isra'ila a matsayin ramuwar gayya kan harin da ta kai ofishin jakadancinta da ke Syria
- Majiyar Saudiyya ta shaidawa Arabiyya cewa babu inda aka wallafa a kasar cewa ta taimakawa Isra'ila wajen kare kanta daga martanin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Saudiyya - Wata majiya ta musanta cewa kasar Saudiyya ta taimaka wajen kakkabo wasu daga daga cikin jirage marasa matuka da kasar Iran ta harba kasar Isra’ila.
Wasu kafafen Isra’ila sun ruwaito yadda wani jami’in gwamnatin Saudiyya ke cewa sun taimaka wajen kare harin da Iran ta kai musu.
A labarin da Arab News ta wallafa, wani jami’in gwamnatin Saudiyya ya musanta cewa kasar ta taimaki Isra’ila wajen kare harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalaman majiyar wacce ta yi magana da Al Arabiyya, babu inda aka ga shaidar Saudiyya ta tallafawa Isra’ila.
“Babu wani shafi da ya wallafa jawabin Saudiyya ta tallafa wajen kare harin akan Isra’ila,” kamar yadda Al Arabiyya ya wallafa.
Iran ta yi martani kan Isra'ila
A makon da ya gabata ne Iran ta harba daruruwan jirage marasa matuka cikin yankin da Isra'ila ta mamaye wanda ya koma cikin kasar.
Harin na zuwa a matsayin martani kan harin da Isra'ila ta kai ofishin jakadancin Iran da ke Damascus na kasar Syria.
Daruruwan jiragen da Iran ta harba kan Isra'ila dai na zuwa a matsayin ramuwa kan manyan laifukan da kasar ta zargi Isra'ila da aikawata, kamar yadda Aljazeera English ta ruwaito.
Fargabar barkewar yaki a gabas ta tsakiya
A wani labarin, tun bayan da kasar Isra'ila ta kai hari kan ofishin jakadancin Iran a Syria ne dai ake ta dar-dar a Gabas ta Tsakiya kan yiwuwar barkewar yaki a yankin.
Bayan kai harin ne hukumomin Iran suka ce za su dauki matakin ramuwa, wanda kuma ta cika alwashin a ranar Asabar din da ta gabata.
Amurka da ke goyon bayan Iran tuni ta gargadi kasar da da kada ta kai wani harin kan Iran domin gujewa tashin hankali.
Asali: Legit.ng