Jerin Kasashe 10 Masu Mafi Munin Shugabanci a Afrika a Shekarar 2024

Jerin Kasashe 10 Masu Mafi Munin Shugabanci a Afrika a Shekarar 2024

World Economics, wata kungiya da ke binciken tattalin arziki daga kasar Birtaniya, ta fitar da jadawalin 2024 na kasashen Afrika mafi kyawun shugabanci, da kuma kasashen da ba su yi dacen gwamnati mai kyau ba.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Fitar da jadawalin shugabanci na kasashe kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito, ya dogara ne bisa abubuwa hudu.

Jadawalin kasashen Afrika da masu karfi da rauni a shugabanci
Kasar Libya ta zama ta 1 a jerin kasashen Afrika da ba su yi dacen gwamnati a 2024 ba. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Abubuwan da ake kallo sun hada da, auna mizanin cin hanci da rashawa; bin dokokin kasa; 'yancin yada labarai da 'yancin yin siyasa.

A wannan jadawalin na 2024 da World Economics ta fitar, ta tattara jerin kasashe 10 na Afrika da ba su yi dacen shugabanni na gari ba.

Kara karanta wannan

Jerin ƙasashen Afirka 12 da tarin basussuka ya masu katutu kuma ya zama barazana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin kasashe mafi munin shugabanci

  1. Libiya (15.4)
  2. Dr Congo (21.6)
  3. Chadi (23.2)
  4. Burundi (24.4)
  5. Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (25.1)
  6. Kamaru (27.2)
  7. Jamhuriyar Congo (28.4)
  8. Misira (28.8)
  9. Zimbabwe (29.0)
  10. Eswatini (30.5)

A hannu daya kuma, binciken World Economics ya nuna cewa ƙasar Mauritius ce ta fi ko ina dacen shugabanci a 2024.

Kasashe 10 mafi kyawun shugabanci

  1. Mauritius (69.3)
  2. Namibiya (69.1)
  3. Afrika ta Kudu (65.5)
  4. Bostwana (65.1)
  5. Ghana (61.7)
  6. Senegal (53.6)
  7. Malawi (52.9)
  8. Lesotho (52.3)
  9. Burkina Faso (51.8)
  10. Gambiya (50.6)

Ina Najeriya ta shige a kasashen?

Duba da cewa ba a ga sunan Najeriya a jerin 10 na kasashe mafi muni ko kyawun shugabanci ba, Legit Hausa ta binciko matsayin ƙasar a wannan jadawali.

Najeriya na a tsaka tsakiya, kasancewar tana da maki 37.0 a bangaren shugabanci, sannan karfin yaki da cin hanci da rashawa na kasar ya yi kasa sosai zuwa maki 27.8.

Kara karanta wannan

Jerin manyan mata 10 mafi arziki a duniya da adadin kudin da suka mallaka

Amma a bangaren samun 'yancin yin siyasa, Najeriya na da maki 53.5, sannan tana da maki 30.9 da kuma 36.8 a bangaren bin doka da kuma 'yancin yada labarai.

Kasashe 20 mafi farin ciki a duniya

A wani rahoton, Legit Hausa ta ruwaito cewa kasashe 20 sun shiga jerin mafi farin ciki a duniya ta fuskar shugabanci, tattalin arziki da tsaro.

A wannan karon ma kasar Finland ce ta zo ta daya a jerin kasashe mafi farin ciki, yayin da Najeriya ta gaza shiga jerin 20 ɗin farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.