An Shiga Jimami Bayan Mutuwar Wanda Ya Fi Kowa Daɗewa a Duniya da Shekaru 114
- An tabbatar da mutuwar Juan Vicente Perez Mora, dattijon da ya fi kowa dadewa a duniya da shekaru 114
- Juan Mora ya rasu ne a jiya Talata 2 ga watan Afrilu a kasar Venezuela bayan ya sha fama da jinya mai tsawo
- Kundin bajintar Guinness ya ba shi lambar yabo a matsayin wanda ya fi kowa dadewa a duniya a shekarar 2022 ya na da shekaru 112
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Venezuela - An shiga jimami bayan rasuwar wanda ya fi kowa dadewa a duniya, Juan Vicente Perez Mora.
Marigayin wanda ɗan ƙasar Venezuela ne ya rasu a jiya Talata 2 ga watan Afrilu ya na da shekaru 144 a duniya.
Mora ya samu lambar yabo daga Guinness
Mora ya samu lambar yabo daga kundin bajinta na Guinness a matsayin wanda ya fi kowa dadewa a duniya a shekarar 2022.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Perez ya zama wanda ya fi kowa dadewa a watan Faburairun 2022 lokacin ya na da shekaru 112, cewar kundin bajinta na Guinness.
Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro shi ma ya tabbatar da mutuwar Mora a shafinsa na X a jiya Talata 2 ga watan Afrilu.
Yawan iyalai da marigayin ya tara a duniya
Marigayin a shekarar 2022 ya na da 'ya'ya 11 da jikoki 41 da 'ya'yan jikoki 18 da tattaba kunne guda 18 a duniya.
An haifi Marigayin wanda manomi ne a ranar 27 ga watan Mayun 1909 a yankin El Cobre da ke jihar Tachira.
Yayin da ya kai shekaru biyar a duniya, Mora ya fara zuwa gonar rake tare da mahaifinsa da kuma yayansa.
Daga bisani Mora ya zama dattijo a yankin wanda ya ba da gudunmawa wurin dinke duk wani rikici da ya taso kama daga na iyalai da filaye da sauransu.
Shugabannin Afrika da suka fi dadewa
A wani labarin, akwai shugabannin kasashen Afirka a da suka fi dadewa a kan kujerar mulkin kasashensu daban-daban.
Wannan rahoto ya kawo muku jerin shugabannin da suka hada da na Kamaru da Equatorial Guinea da Jamhuriyar Dimukradiyya ta Congo.
Asali: Legit.ng