Mutumin da yafi dadewa a Duniya mai shekaru 145.

Mutumin da yafi dadewa a Duniya mai shekaru 145.

Jami’an kasar Indonesiya sun bayyana hoton mutumin da yafi shekaru a duniya da har ma ya kosa ya mutu, mai suna Mbah Gotho da ake ganin shekarunsa na haihuwa sun kai 145.

Mutumin da yafi dadewa a Duniya mai shekaru 145.

Kamar yadda takardun haihuwarsa suka nuna, an haifi Gotho ne a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 1870, sa’annan rahotanni sun nuna duk kannensa goma da matanshi hudu duk sun mutu sun barshi da rai.

A wani hira da jaridar UK Mirror tayi da tsohon a kauyen su na Sragen a yankin Central Java yace wani dare ne jemage bai gani ba? Don haka ba zai damu ba idan ya mutu a yau. Yace “abin da nake so kadai a yanzu shine in mutu, jikokina duk sun manyanta, sun yi arziki” da aka tambayeshi sirrin tsawon raid a yayi, sai yace “hakuri ne sirrin tsawon rai.”

Daya daga cikin jikokin Gotho yace kakansa ya dade yana jiran mutuwa tun yana da shekaru 122, amma har yau bata riske shi ba, yace “wannan kabarin da ka gani a nan, tun 1992 muka yi shi, shekaru 24 da suka wuce kenan”

Ya kara da cewa, a yan kwanakinnan a baki ake ba kakan nasa abinci, sa’annan a mai wanka, sai ya saurari rediyo sakamakon baya iya kallon talabijin saboda idon sa ya lalace.

Jami’an ofishin tara kundin tarihin kasar Indonesiya sun tabbatar da 31 ga watan disamba 1870 a matsayin ranar haihuwar Gotho, dake rubuce a kan katin sa na shedar dan kasa. Sun kara da cewa, tuni danginsa suka gina masa kabari a gefen kaburburan yayansa.

Wannan tsohon mutuwa kawai yake nema ido rufe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel