Rai da Ajali: An Shiga Jimami Yayin da Sarki Mafi Dadewa a Jihar Ribas Ya Kwanta Dama

Rai da Ajali: An Shiga Jimami Yayin da Sarki Mafi Dadewa a Jihar Ribas Ya Kwanta Dama

  • Rahoton da muke samu daga jihar Ribas ya labarta rasuwar basaraken gargajiya mafi dadewa a jihar
  • Wannan na zuwa ne daga bakin dan mamacin, inda yace za a sanar da al’umma sauran shirye-shiryen da ake
  • Najeriya na rasa sarakuna da masu rike da sarautun gargajiya a lokuta mabambanta a cikin ‘yan shekarun da suka gabata

Jihar Ribas - Fitaccen basaraken gargajiya mafi dadewa a jihar Ribas, Prince TJT Princewill, Amachree XI, Amanyanabo na masarautar Kalabari ya rasu, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake tabbatar da rasuwar shahararren uban kasar a birnin Fatakwal a ranar Asabar, dan marigayin, Prince Tonye Princewill, ya ce mahaifin nasa tabbas ya rasu salin-alin.

Princewill ya ce an sanar da Majalisar Sarakunan Buguma da Majalisar Sarakunan Kalabari game da rasuwar mahaifin nasa bisa abin da al’adar Kalabari ta tanada.

Kara karanta wannan

Dan Majalisa A Bauchi, Ado Wakili, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Kwanaki 3 Kafin Wa'adinsa Ya Kare

Allah ya yiwa basarake rasuwa
Barasake mafi dadewa a Ribas, wanda ya rasu | Hoto: Prince Tonye Princewill
Asali: Facebook

Wani hali ake ciki bayan rasuwar basaraken?

Princewill, tsohon dan takarar gwamna na rusasshiyar jam’iyyar AC a jihar Ribas ya ce sanarwar da ya fitar ta rasuwar basaraken za a iya daukarta a matsayin sanar da duniya a hukumance game da rasuwar mahaifinsa, Daily Independent ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Princewill ya bayyana a cikin sanarwar cewa:

"Za a kara fitar da sanarwa a cikin kwanaki ko makwanni masu zuwa, amma muna barar addu'o'inku da fatan alheri, ba kawai ga iyalinsa ba, har ma ga daukacin masarautar Kalabari."

A hankali, Najeriya na ci gaba da rasa manyan sarakunanta, inda da yawan masarautun ke komawa hannun ‘ya’ya da jikoki na sarakunan.

A shekarar da ta gabata, rahotanni da dama sun fito na rasuwar sarakuna a yankunan Arewa da Kudancin Najeriya.

Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Babban Basarake Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Yana da Shekara 87

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Imo Ya Rasu

A wani labarin, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da cewa shugaban hukumar Egbe Idimu LCDA, ya sanar da mutuwar Onidimu na ƙasar Idimu, Oba Azeez Dada Aluko Olugoke.

A cikin wata sanarwa ranar Lahadi, 14 ga watan Mayun 2023, wacce shugaban hukumar Egbe Idimu LCDA, Sanyaolu Olowoopejo, ya fitar, ya bayyana cewa Oba Olugoke, ya mutu ne da safiyar ranar Lahadi bayan yayi fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya.

Olowoopejo ya kuma cigaba da cewa, iyalan mamacin za su sanar da lokacin binne shi nan ba da daɗewa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.