Fargaba Yayin da Tsohon Shugaban Kasa Ya Gamu da Mummunan Hatsarin Mota
- An shiga fargaba bayan tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya gamu da tsautsayin hatsarin mota
- Zuma ya gamu da iftila'in ne a yau Juma'a 29 ga watan Maris inda motarsa ta ci karo da ta direban babbar mota
- Rundunar 'yan sanda a kasar ta tabbatar da haka inda ta ce an cafke direban mai shekaru 51 a duniya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Afirka ta Kudu - Tsohon shugaban kasar Afirka, Jacob Zuma ya gani da mummunan hatsarin mota.
Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 27 ga watan Maris yayin da wani direban babban mota ya ci karo da shi.
Yadda Jacob Zuma ya gamu da hatsari
Rundunar 'yan sanda a kasar (SAPS) ita tabbatar da haka a yau Juma'a 28 ga watan Maris a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ta ce direban babbar mota ne ya ci karo da motar sulke da ke ɗauke tsohon shugaban kasar.
Sai dai Zuma da masu tsaronsa sun yi nasarar tsira ba tare da rauni ba inda aka ɗauki tsohon shugaban kasar mai shekaru 81 zuwa gidansa.
An cafke direban da ya kara da Zuma
Yan sanda sun sanar da kama direban mai shekaru 51 kan zargin sakaci a tuki da kuma kasancewa cikin maye.
Ana sa ran direban zai gurfana a gaban kotu a ranar Talata 2 ga watan Afrilu na wannan shekara da muke ciki.
Wannan hatsari da ya faru watanni kadan kafin zabe inda ya saka shakku kan akwai wani abu a kasa da zargin ana son ganin bayan Zuma.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar zaben kasar ta dakatar da Zuma daga tsayawa takarar.
Hukumar ta hana tsohon shugaban kasar tsayawa takara a babban zaben da za a gudanar a ranar 29 ga watan Mayu.
Buhari ya yabawa Tinubu da ayyukan alheri
A baya, mun ruwaito muku cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan inganta kasa.
Buhari ya yi yabon ne yayin da ya ke ta ya shugaban murnar zagayowar ranar haihuwarsa a jiya Alhamis 28 ga watan Maris.
A yau Juma'a ne 29 ga watan Maris ya cika shekaru 72 a duniya inda manya-manyan kasar suka ta ya shi murna.
Asali: Legit.ng