Yanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ɗaurin watanni 15 a gidan yari

Yanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ɗaurin watanni 15 a gidan yari

Kotu ta samu tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ta laifin raina kotu ta kuma yanke masa ɗaurin watanni 15 a gidan yari, News Wire ta ruwaito.

An yanke wa Zuma wannan hukuncin ne saboda ƙin amsa sammaci guda biyu da ake aike masa a cewar mataimakin alƙali Sisi Khampepe yayin yanke hukunci a Johannesburg a ranar Talata.

Yanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ɗaurin watanni 15 a gidan yarin
Yanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ɗaurin watanni 15 a gidan yarin
Asali: Original

DUBA WANNAN: Azonto: Gwamnatin Benue ta rushe gidajen kasurgumin mai garkuwa da mutane da ake nema ruwa a jallo

Zuma ya ƙi amsa gayyatar kotu domin amsa tambayoyi game da zargin rashawa da ake zargin an tafka yayin da ya shugabanci kasar na tsawon shekaru tara, The Cable ta ruwaito.

Wannan hukuncin ya biyo bayan shari'ar da ake yi ne tsakanin Zuma da Zondo commission de ke binciken zargin rashawa da aka tafka a lokacin da ya ke shugaban kasa.

KU KARANTA: 'Yan majalisar Zamfara baki ɗayansu za su bi Matawalle zuwa jam'iyyar APC, Hadimin Gwamna

An tursasawa Zuma mai shekaru 79 sauka daga mulki ne a shekarar 2018 saboda zarginsa da aikata rashawa.

Ku saurari ƙarin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel