Matar tsohon Shugban Kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ta yi kararsa a kotu kan kuɗin kula da yara

Matar tsohon Shugban Kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ta yi kararsa a kotu kan kuɗin kula da yara

Nqabayethu Buthelezi, lauyan tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya wakilce shi a kotu a ranar Talata 18 ga watan Agusta bayan matarsa ta uku, Tiobeka Madiba ta yi kararsa a kotu kan rashin kudin kula da ita da yar ta.

Tobeka ta yi karar Zuma a kotun Majistare da ke Durban inda ta ke neman ya rika biyan ta R14 000 duk wata a matsayin kudin kula da yar su mai shekaru 14.

Sai dai shugaban lauyoyin Zuma, Eric Mabuza ya musanta cewa tsohon shugaban kasar ba ya bada kudin kula da yarsa mai shekaru 14.

Matar tsohon Shugban Kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ta yi kararsa a kotu kan kudin kula da yara
Matar tsohon Shugban Kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ta yi kararsa a kotu kan kudin kula da yara. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

Mabuza a yayin da ya ke musanta ikirarin ne tsohuwar matar shugaban kasar na cewa ba ya kula da yar sa tun bayan rabuwarsu a farkon wannan shekarar ya fada wa kotu cewa Tobeka ta dena aiki tun shekaru 14 da suka wuce bayan haihuwar yar su.

DUBA WANNAN: Shugaban kasar Portugal ya fada cikin ruwa ya ceto mata biyu (Hotuna)

An kammala sauraron korafin ba tare da cimma wata matsaya ba. Lauyoyi masu kare Zuma, Nqaba Buthelezi da Rudolph Mbalula sun ki cewa komi a kan lamarin.

Tobeka ita ma ba ta yi wani tsokaci ba saboda wasu dogaran fadar shugaban kasa sun tafi da ita ta kofar baya.

Mai bincike, Thulasizwe Mahlobo ya ce abinda zai iya cewa a yanzu kawai shine bangarorin biyu sun zo kotun ne domin yin sulhu amma ba wai wata sharia ba.

Ya ce;

"Kawai sulhu ake yi a kan wasu batutuwa da suka taso, muna neman ganin yadda za a daidaita ne ... ni jagoranci kawai na ke yi.

"Duba da cewa jagoranci na ke yi, ba ni da ikon bayar da wani bayani a halin yanzu har sai lauyoyin bangarorin biyu sun gamsu da yarjejeniyar da suka amince."

Mahlobo ya kara da cewa bangarorin biyu za su sake dawo wa nan gaba domin karasa tataunawar.

Ya ce;

"Za su dawo. Bangarorin biyu za su tafi su tuntubi wadanda suke kare wa (Zuma da Madiba) sannan su dawo wuri na. Daga nan sai mu dauki mataki na karshe idan mun hadu.

"Babu wani abu da aka tattauna kafin yanzu, bangarorin biyu za su gabatar da korafinsu saboda mu yi sulhu. Wannan shine dalilin taron."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel