Haifaffen Najeriya da Ya Zama Sojan Amurka Ya Rasa Ransa a Teku, Bayanai Sun Fito

Haifaffen Najeriya da Ya Zama Sojan Amurka Ya Rasa Ransa a Teku, Bayanai Sun Fito

  • Rahotanni sun bayyana cewa, wani sojan ruwa haifaffen Najeriya da ke kasar Amurka, Michael Aregbesola, ya rasu
  • Jami'in sojan ruwan ɗan asalin Najeriya ya mutu a cikin tekun Bahar Maliya bayan ya faɗa cikin ruwa yayin da yake aiki
  • Rundunar sojin ruwan Amurka ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, a wata sanarwa da ta fitar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ƙasar Amurka - Wani jami’in sojan ruwa na Amurka, haifaffen Najeriya, Michael Aregbesola, ya mutu a tekun Bahar Maliya bayan ya faɗo a cikin ruwa yayin da yake aiki.

Jaridar The Punch ta ce rundunar sojojin ruwan Amurka ta tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 23 ga watan Maris 2024.

Kara karanta wannan

Bauchi: Adadin mutanen da suka mutu a wurin rabon zakkah ya ƙaru, an faɗi sunayensu

Sojan ruwan Amurka ya mutu a teku
Michael Aregbesola ya rasu bayan ya fado cikin teku Hoto: @OrissAreg_ (Orie Areg)
Asali: Twitter

A cewar rundunar sojan ruwa ta Amurka, Aregbosola yana aiki ne da tawagar "Swamp Foxes" a ƙarƙashin 'Helicopter Maritime Strike Squadron (HSM) 74'.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar sojin ruwa ta kuma yaba da ƙwazon da ya nuna a wajen aikinsa.

Wani ɓangare na sanarwar da rundunar sojojin ruwan ta fitar na cewa:

"Aregbesola ya cika dukkanin jarumtaka da ƙwazon da ake nema daga matuƙin jirgin rundunar sojojin ruwan Amurka.
"Ƙwazon da ya nuna kafin a tura shi fagen daga da bayan an tura shi, ya wuce yin gyaran jirgi, ya kasance mai mutunta dukkanin ƴan tawagarsa."

Wanene Michael Aregbesola?

Aregebesola ɗan Najeriya ne wanda ya zama abin magana a shekarar 2020 bayan ya bar Najeriya domin shiga rundunar sojin ruwa ta Amurka.

Ya yi iƙirarin cewa rundunar ta hango akwai abin mora a tattare da shi, inda ta mayar da shi matuƙin jirgin ruwa.

Kara karanta wannan

Tsadar iskar gas: Jigon APC ya bukaci Shugaba Tinubu ya tausayawa talaka

Ya bayyana hakan ne dai a wani rubutu da ya yi a wancan lokacin a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

A kalamansa:

"Na kwashe shekaru ba ni da aikin yi, ƙasata ta haihuwa (Najeriya, wacce yanzu na bar ta) ta kasa share min hawaye, amma rundunar sojojin ruwan Amurka ta hango abin mora a tattare da ni sannan ta mayar da ni matuƙin jirgi, ina aiki a ɓangaren jirage."

Sojan Amurka ya bar duniya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani sojan Amurka ya yanke shawarar salwantar da ransa domin barin duniya.

Aaron Bushnell mai shekara 25 a duniya ya ɗauki wannan matakin domin nuna adawa da kisan kiyashin da Isra'ila ke ƴi wa Falasɗinawa a zirin gaza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng