Jita-Jitar Siyasa Yayin da El-Rufai Ya Ziyarci Tsohon Minista a Najeriya, an Yada Hotunan

Jita-Jitar Siyasa Yayin da El-Rufai Ya Ziyarci Tsohon Minista a Najeriya, an Yada Hotunan

  • Babban 'dan siyasa kuma 'dan APC, Femi Fani-Kayode ya yi magana kan ziyarar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya kai masa
  • Tsohon Ministan jiragen ya bayyana El-Rufai a matsayin kwaro a siyasar Najeriya wanda ya taka rawar gani na fiye da shekaru 23
  • Fani-Kayode ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Juma’a 15 ga watan Maris inda ya ce ya ji dadin ziyarar tsohon gwamnan Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya ziyarci tsohon Ministan sufuri, Femi Fani-Kayode.

Femi Fani-Kayode shi ne kakakin kamfe na zaben shugaban kasa a shekarar 2023 da ta gabata wanda Bola Tinubu ya yi nasara.

Kara karanta wannan

Kakakin kwamitin kamfen Atiku ya faɗi muhimman abubuwa 2 da Najeriya ke buƙata kafin zaɓen 2027

Hotunan yadda tsohon gwamna El-Rufai ya kai wa tsohon Minista ziyara
Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya kai ziyara gidan tsohon Minista, Fani-Kayode. Hoto: Femi Fani-Kayode.
Asali: Twitter

Fani-Kayode ya yabawa El-Rufai a siyasa

Fani-Kayode ya bayyana ziyarar ne a yau Juma’a 15 ga watan Maris a shafinsa na X inda ya yada hotunansu tare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan na Olusegun Obasanjo ya bayyana El-Rufai a matsayin wani gwaska a siyasar Najeriya baki daya.

El-Rufai ya taka rawar gani a zaben da aka gudanar wanda ya ba Shugaba Tinubu nasarar zama shugaban kasa.

Sai dai bayan Tinubu ya yi niyyar saka masa da kujerar Minista, ya samu tasgaro yayin da Majalisar Dattawa ta ki tantance shi.

Har ila yau, wannan ziyara ta saka ayar tambaya saboda ba a saba ganinsu tare ba bare kuma a ce har ta kai sun ziyarci juna.

Abubuwan da El-Rufai, FFK suka tattauna

Wannan ziyara na zuwa ne yayin da ‘yan siyasa ke ta faman shirye-shiryen siyasar 2027 da kuma layin da za su kama.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauko mutumin Buhari ya ba shi shugabancin hukumar kula da almajirai

“Tsohon gwamnan Kaduna kuma tsohon Ministan Abuja, Nasir El-Rufai ya zo gida na a wannan yammaci.”
“Mun tattauna batutuwan da suka shafi Najeriya, Mallam gwaska ne a siyasar Najeriya wanda ya yi rawar gani a cikinta fiye da shekaru 23.”

- Femi Fani-Kayode

Bello El-Rufai ya yi magana kan mahaifinsa

Kun ji cewa dan Majalisar Tarayya a Kaduna, Bello El-Rufai ya ce mahaifinsa bai taba son kujerar Minista ba.

Bello ya ce sai da suka ba tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai hakuri kafin ya amince da karbar kujerar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.