Dani Alves Ya Kashe Kansa Bayan Yanke Masa Hukunci a Gidan Yari? An Bayyana Gaskiyar Lamarin
- A jiya Asabar ce 9 ga watan Maris aka yi ta yada cewa tsohon dan wasan Barcelona ya yi ajalin kansa a gidan yari
- Wani dan jarida daga Brazil mai suna Paulo Albuquerque shi ya fara yada rahoton inda daga bisani wasu jaridu suka dauka
- Sai dai dan uwan dan wasan, Ney Alves ya karyata jita-jitar da ake yadawa inda ya ce su na tunanin daukar matakin shari’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Yayin da ake ta yada labarin cewa Dani Alves ya kashe kansa a gidan yari, dan uwan tsohon dan wasan Barcelona ya yi martani kan lamarin.
Ney Alves ya karyata jita-jitar da ake yadawa a shafin Instagram inda ya ce labarin ba shi da tushe bare makama inda ya nuna damuwa kan lamarin.
Matakin da Ney zai dauka kan labarin Alves
Ney ya ce su na tunanin daukar matakin shari’a kan wannan bata suna musamman kan dan jaridar da ya yada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jiya Asabar ce 9 ga watan Maris, dan jarida daga Brazil, Paulo Albuquerque ya fara yada labarin kashe kai din Alves a gidan yari.
Wannan na zuwa ne bayan yanke hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari da aka yi wa Alves kan zargin cin zarafin wata budurwa a Spain.
Martanin Ney kan jita-jitar da ake yaɗawa
Da ya ke martani, dan uwan Alves ya ce mutane ba su da tausayi, ya nuna takaici inda ya ce bayan yanke masa hukunci za su bullo da wannan labarin.
“Wane irin rashin tausayi ne ga mutane? An yanke masa hukunci kan zargin alaka da matar da ta shiga makewayi, shin hakan bai isa ba?”
“Babban abin takaici yanzu shi ne su na son ganin bayansa, su na son ganin dan uwana ya mutu, wannan wane irin rashin imani ne?”
- Ney Alves
Kotu ta daure Alves shekaru 4
A baya, mun ruwaito muku cewa wata kotu a kasar Spain ta yankewa tsohon dan wasan Barcelona daurin shekaru hudu a gidan kaso
Ana zargin Alves da cin zarafin wata budurwa ‘yar shekaru 23 a duniya a gidan gala bayan ta shiga makewayi.
Asali: Legit.ng