‘Yan fashi sun kutsa gidajen ‘Yan wasan PSG, sun sacewa Di Maria dukiyar Naira Miliyan 250

‘Yan fashi sun kutsa gidajen ‘Yan wasan PSG, sun sacewa Di Maria dukiyar Naira Miliyan 250

- Wasu ‘yan fashi sun shiga gidan Angel Di Maria sun yi sata a Birnin Faris

- Dole aka cire Di Maria daga wasa a jiya bayan an ji labarin shiga gidansa

- Kafin yanzu an taba auka wa gidajen Icardi, Daniel Alves da Thiago Silva

‘Dan wasan gaban Paris Saint-Germain, Angel Di Maria ya yi rashin sa’a biyu yayin da ‘yan fashi da makami su ka auka gidansa a birnin Faris, Faransa.

Rahotanni daga gidan jaridar AFP sun bayyana cewa an shiga gidan tauraron bayan Paris Saint-Germain ta sha kashi a hannun Nantes a ranar Lahadi.

‘Yan fashin sun sace agogo da kuma wasu kayan kyale-kyale masu tsada a gidan ‘dan kwallon na kasar Argentina da ke yammacin babban birnin Farisa.

Kamar yadda AFP ta rahoto, wadannan barayi ba su yi wa kowa ta’adi a gidan ‘dan wasan ba.

KU KARANTA: Mikel Obi ne gaba a sahun gawurtattun Attajiran ‘Yan wasa 10

‘Dan kwallon bai kawo wa ‘yan sanda kara da aka shiga gidan na sa ba. ‘Dan wasan ya isa gidan a lokacin da aka shiga, amma bai iya ganin barayin ba.

Wani jami’in tsaro ya ke cewa: “Ba su ji komai ba a lokacin da su ka zazzage wani akwatin dukiya da ke boye a saman benen gidan na sa da ke Neuilly.”

“Ba ayi lissafin darajar dukiyar da su ka sace ba, amma an ce bai kai Dala 600, 00 ba. Idan aka yi lissafin wannan kudi a Naira, sun kusa Naira miliyan 250.

Bayan haka an shiga gidan ‘dan wasan bayan kasar Brazil na kungiyar ta PSG, Marquinhos.

‘Yan fashi sun kutsa gidajen ‘Yan wasan PSG, sun sacewa Di Maria dukiyar Naira Miliyan 250
Di Maria da Marquinhos Hoto: www.elfutbolero.us
Asali: UGC

KU KARANTA: Davido ya ajiye adawa a gefe, ya taya Wiz Kid da Burna Boy murna

A watan jiya an yi sata a gidan Mauro Icardi, kafin nan an taba shiga gidajen su Thiago Silva, Dani Alves da Eric Maxim Choupo-Moting a PSG an yi sata.

A baya kun ji cewa Yarima Abdullah bin Mosaad na kasar Saudiyya ya na shirin sayen wata kungiyar kwallon kafa da ake kira Chateauroux a Faransa.

A halin yanzu Abdullahi yana da kungiyoyi da suka hada da Sheffield United, Beerschot a Belgium, Kerala United a Indiya da Al Hilal United ta UAE.

Yarima Abdullahi yana fatar kungiyar za ta farfado nan gaba duk da cewa yanzu tana kasan tebur.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel