Kungiyar Barcelona za ta saida wasu ‘yan wasan ta

Kungiyar Barcelona za ta saida wasu ‘yan wasan ta

 

– Rashin kudi ya sa Kungiyar Barcelona za ta saida wasu daga cikin ‘yan wasan ta.

– Watakila a saida Arda Turan da kuma Carlos Bravo a kakar bana.

– Kungiyar dai ba za ta rasa wadanda za su maye gurbin na su ba.

Kungiyar Barcelona za ta saida wasu ‘yan wasan ta

 

 

 

 

 

Zakarun la-liga, Barcelona ka iya saida ‘yan wasan ta; Arda Turan da kuma Carlos Bravo, domin sayayyar Kungiyar ta wuce lissafin kasafin da doka ta tanada na kowane kasuwa. Kungiyar ta Barcelona dai ta saye yan wasa da dama a kakar bana, wadanda suka hada da; Denis Suarez, Samuel Umtiti, Lucas Digne da kuma Andre Gomes. Wannan ya sa asusun kungiyar yayi kar-kaf. Duba da haka, kuma yan wasa irin su Neymar Jr. da kuma Sergio Busquets sun sabunta kwantiragin su da Kungiyar, wannan ya kara sa Kungiyar sai tayi da gaske.

Kungiyar dai har wa yau, tana bukatar wani dan wasa (na gaba) wanda za ayi amfani da shi idan har babu daya daga cikin; Messi Lionel, Neymar Jr. ko Luis Suarez. Kungiyar dai ba ta samu wani abin shiga ba daga cinikin Dani Alves zuwa Juventus. Haka ma dai ba wani abin a zo a ganin aka samu ba wajen saida Alen Halilovic da Marc Batra zuwa Hamburg da kuma Borussia Dortmund. Wannan ya sa idan dai har Kungiyar na bukatar kudi, sai ta saida Arda Turan zuwa ga Kungiyar Arsenal da kuma Carlos Bravo, wanda tsohon Kocin Kungiyar, Pep Guardiola na Man City ke neman sa.

KU KARANTA: WANNAN DAN WASAN ZAI BAR KULOB DIN SA

Idan dai har Kungiyar ta Barcelona ta saida wadannan yan wasa, ba za ta rasa wadanda za su maye gibin da suka bari ba. Kungiyar na da yan wasan tsakiya barkatai, da kuma gola Marc Andre Ter Stegen maimakon Carlos Bravo.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: