Yar Majalisa Ta Yi Murabus Bayan Bidiyo Ya Kamata Tana ‘Satar’ Jaka a Kanti
- Yar majalisar dokokin kasar New Zealand karkashin jam'iyyar Green Party ta yi murabus biyo bayan kama ta tana satar jakar hannu
- Rahotanni sun bayyana cewa an sha yi wa 'yar majalisar mai suna Golriz Ghahraman zargin yin sace-sace a kantunan sayar da kayayyaki
- Sai dai wannan karon, wani faifan bidiyo ya nuna yadda 'yar majalisar ta saci jakar hannu a wani kanti, lamarin da ya sa ta yi murabus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wata 'yar majalisar dokokin kasar New Zealand Golriz Ghahraman ta yi murabus a ranar Talata, sakamakon zarge-zargen satar kayayyaki a kantunan siyayya.
Ghahraman, ta kasance 'yar gudun hijira ta farko da aka zaba a majalisar dokokin New Zealand a jam'iyyar Green Party.
Ana zargin Ghahraman da yin sata har sau uku a shagunan tufafi guda biyu, daya a Auckland dayan kuma a Wellington, Arise News ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama 'yar majalisar dumu-dumu tana satar jakar hannu
Ta ce damuwa da ke da alaka da aikinta ne ya sa ta "yin abubuwan da suka saba da ɗabi'arta kwata-kwata".
Tsohuwar lauyar kare hakkin dan Adam a Majalisar Dinkin Duniya ta kafa tarihi a shekarar 2017 inda ta zama yar gudun hijira ta farko da aka rantsar a cikin gwamnatin New Zealand.
The Guardian ta ruwaito cewa murabus da Ghahraman ta yi a ranar Talata ya zo ne bayan faifan CCTV ya fito da ke nuna yadda ta dauki jakar hannu daga wani kantin Auckland.
Jam'iyyar Green Party ta yi martani kan murabus din Ghahraman
'Yar shekaru 43, wacce ba a tuhume ta da wani laifi ba, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce abin da ta yi ya yi muni kan kyawawan dabi'un da jama'a ke tsammani daga zababbun wakilai.
Da yake mayar da martani kan murabus din nata, shugabar jam'iyyar Green Party, James Shaw ya ce Ghahraman ta kasance tana fuskantar "barazanar cin zarafi, tashin hankali, barazanar kisa tun ranar da aka zabe ta a majalisar dokoki".
Kaduna: Yan bindiga sun tsare wanda ya je kai masu kudin fansa
A wani labarin kuma, wani tsohon shugaban makaranta ya shiga hannun 'yan bindiga bayan da ya je kai masu kudin fansar wani da suka yi garkuwa da shi.
An ruwaito cewa kwanaki uku kenan da masu garkuwar suka tsare malamin dan asalin garin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, kuma sun nemi kudin fansa daga iyalansa.
Asali: Legit.ng