Hotuna Sun Yadu Yayin da Shugaban Kasa Ya Raba Kekuna Ga Hakimai Matsayin Kyautar Kirsimeti
- An caccaki shugaban ƙasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa saboda ba Hakimai kekuna a matsayin kyautar Kirsimeti
- Wasu da dama a shafukan sada zumunta sun bayyana kyautar a matsayin abin kunya yayin da hotunan taron ke ci gaba da yaɗuwa
- Uwargidan shugaban ƙasa Amai Auxillia Mnangagwa ita ma ta ba da gudunmawar abubuwan bikin Kirsimeti ga matan ƙauyen
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Zvishavane, Zimbabwe - An san lokacin Kirsimeti a matsayin lokacin bayar da kyauta da murna, wanda abin da shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya yi ke nan ta hanyar ba da gudunmawar kekuna 54 ga Hakimai.
Ma'aikatar yaɗa labarai ta ƙasar ta sanar da hakan ta shafinta na X (wanda aka fi sani da Twitter) @InfoMinZW, a ranar Talata, 26 ga Disamba.
A cewar sanarwar, Shugaba Mnangagwa ya ba da kyautar kekunan ga Cif Mapanzure, a makarantar firamare ta Lundi da ke Zvishavane, wanda zai raba wa sauran Hakiman.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Uwargidan shugaban ƙasa Amai Auxillia Mnangagwa ta kuma ba wa matan ƙauyen kyaututtukan Kirsimeti.
Sanarwar na cewa:
"A yau, mai girma shugaban ƙasa Mnangagwa @edmnangagwa ya ba da gudunmawar kekuna 54 ga Cif Mapanzure, a makarantar firamare ta Lundi da ke Zvishavane. Za a raba kekunan ga Hakiman ƙauyukan.
"Har ila yau a wajen, akwai uwargidan shugaban ƙasa, Amai Auxillia Mnangagwa, wacce ta ba da gudunmawar kyaututtukan Kirsimeti ga matan Hakiman ƙauyukan da suka halarci taron."
Ƴan soshiyal midiya sun yi martani
An cigaba da mayar da martani dangane da gudunmawar kekuna 54 da aka ba Hakiman ƙauyuka a Zimbabwe a matsayin kyautar Kirsimeti.
Ga kaɗan daga ciki:
@SinatraGunda ya rubuta:
"Ku cire wannan, abin kunya ne. Kekuna 54 da kuma kuɗin da za ku aika da tawagar ku zuwa wajen, shin ku na yin nazari kuwa?
@ SimonTshuma1 ya rubuta:
"A wannan zamani har yanzu ana raba kekuna. Na tabbata shugaban ƙasa zai iya ba da kyautar Honda ga kowane Hakimi a ƙasar."
@NdeteStanley ya rubuta:
"Nagode da karamcin da kakeyi, shugaban kasa.. Allah ya baka ikon cigaba da kyautatawa."
Shugaban Zimbabwe Ya Ba Dansa Mukami
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya ba ɗan cikinsa David Kudakwshe Mnangagwa muƙami.
Shugaban ƙasar ya kuma ba wani ɗan'uwansa muƙamin minista a ƙasar ta Zimbabwe.
Asali: Legit.ng