Tsohon shugaban kasar Zimbabwe Mugabe baya iya tafiya
Tsohon shugaban kasar Zimbabwe Mugabe, mai shekara 94 baya iya tafiya saboda halin rashin lafiya, shugaban kasa Emmerson Mnangagwa ya bayyana.
Ya kara da cewa, Mista Mugabe na a kasar Singapore inda yake jinyar wani rashin lafiya da ba’a bayyana ba tsawon watanni biyu da suka gabata.
Tsohon shugaban kasar ya yi tafiye-tafiye da dama don neman lafiya gabannin barinsa mulki.
Mista Mnangagwa ya zama shugaban kasa shekara daya da ya gabata bayan barin Mugabe mulki sakamakon sanya baki da soji ta yi.
A lokacin Mugabe nada shekara 37 akan mulki, farko a matsayin Firaye minister, sannan kuma shugaban kasa.
KU KARANTA KUMA: Kada ka ji komai za mu kawo maka kuri’u miliyan 15 – Kungiyar mata da matasan Arewa maso kudu
Shi ya jagoranci fafutukar yan Zimbabwe na samun yancin kai daga hannun turawa marasa rinjaye.
Shugaba Mnangagwa na jawabi ne ga wani gangami a garin tsohon shugaban kasar lokacin da yayi Magana akan lafiyar nasa.
Ya ce duk da cewar baya iya tafiya, tsohon shugaban kasar na samun sauki sosai kuma zai koma kasar a mako mai zuwa.
Gwamnati ce kuma ke biyan kudaden maganin shi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng