Shugaban Kasa Ya Ruguza Majalisa da Aka Yi Sabon Yunkurin Juyin Mulki a Afrika

Shugaban Kasa Ya Ruguza Majalisa da Aka Yi Sabon Yunkurin Juyin Mulki a Afrika

  • Umaro Sissoco Embalo ya zargi sojoji da yunkurin yin juyin mulki a Guinea-Bissau, saboda haka ya ruguza majalisar tarayya
  • Shugaban kasar Guinea-Bissau ya sake daukar irin matakin da ya dauka a 2022, wannan karo ‘yan adawarsa sun huro masa wuta
  • Ana rigima a kasar Afrikan tsakanin sojojin fadar shugaban kasa da sojojin da ke karkashin ikon majalisar da ke hannun ‘yan adawa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Guinea-Bissau – Shugaba Umaro Sissoco Embalo na kasar Guinea-Bissau ya rusa majalisa a kan zargin yunkurin hambarar da gwamnati.

Rahoton Reuters ya ce Umaro Sissoco Embalo ya kawo wata doka wanda ta ruguza majalisar Guinea-Bissau, ya na cewa za ayi juyin mulki.

Guinea-Bissau
Shugaban Najeriya a Guinea-Bissau Hoto:Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

An sauke 'yan majalisa saboda juyin mulki

Kara karanta wannan

NPA v Intel: Dalilin maidawa tsohon kamfanin Atiku kwangila da Tinubu ya hau mulki

A ranar Litinin ne shugaban kasar Afrikan ya kawo dokar da ta bar al’ummarsa babu majalisar da ke kafa dokoki da zurawa masu mulki ido.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ne karo na biyu da aka rusa majalisar tarayya a Guinea-Bissau a shekaru uku.

Mai girma Umaro Sissoco Embalo ya jefa kasarsa cikin rudani, ya kuma ce za a gudanar da zabe nan gaba, ba tare da ya tsaida wani lokaci ba.

Shugaban kasa zai iya ruguza majalisa?

Domingos Simoes Pereira wanda shi ne shugaban majalisa kuma jagoran jam’iyyar PAIGC da ta samu rinjaye a zaben ‘yan majalisa ya soki lamarin.

An rahoto Domingos Simoes Pereira yana cewa matakin da Embalo ya dauka ya ci karo da doka, bai da ikon rusa majalisar da ta ba ta shekara ba.

Babu zaman lafiya a kasar Guinea-Bissau

Tun a makon jiya ake rikici a Bissau da sojoji su ka fito da wani ministan jam’iyyar adawa da aka tsare ana bincikensa a kan aikata rashin gaskiya.

Kara karanta wannan

"Akwai kotun Allah": Martanin jama'a bayan kotu ta yanke hukunci a shari'ar Abba da Ado Doguwa

France 24 ta ce an saba ganin rikici da juyin mulki tun da Guinea Bissau ta samu ‘yancin kai daga hannun turawan kasar Portugal a shekarar 1974.

A shekarar 2022, shugaba Embalo ya rufe majalisa da sunan rashin gaskiya da sata bayan nan sai aka ji labari ya kara iko ga wadanda ke tsaronsa.

Sojoji sun kashe mutane a Najeriya

A Najeriya kuma ana da labari tsohon Minista,Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya bukaci ayi bincike a hukunta sojojin da su ka kashe mutane.

Jama’a sun yi kaca-kaca da sojoji a dalilin kuskuren dasa bam ga masu bikin maulidi ganin an taba yin haka a Borno, Yobe, Zamfara da Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng