An Hana Fasinjojin Najeriya 264 da Suka Tashi Daga Kano Shiga Saudiyya Saboda Biza

An Hana Fasinjojin Najeriya 264 da Suka Tashi Daga Kano Shiga Saudiyya Saboda Biza

  • An hana fasinjoji 264 na jirgin Air Peace shiga kasar Saudi Arabiya bayan sun dira Jiddah daga Jihar Kano
  • Hukumomin Saudiyya sun soke bizar dukkan fasinjojin Air Peace a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba
  • An tattaro cewa sai da ofishin jakadancin Najeriya na Saudiyya ya saka baki sannan aka rage yawan fasinjojin zuwa 177

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jeddah, Saudiyya - An shiga dimuwa da mamaki yayin da Hukumomin Saudiyya suka soke bizar dukkan fasinjoji 264 da aka dako daga Kano da Legas a ranar Lahadi.

Jami'an na Saudiyya sun dage cewa jirgin ya mayar da su Najeriya inda ya dako su.

An hana yan Najeriya 264 shiga Saudiyya
An hana fasinjojin Najeriya da suka tashi daga Kano shiga Saudiyya. Hoto: Air Peace
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Zaben Bayelsa: Bayan tattara sakamakon kananan hukumomi, an fadi wanda ke kan gaba da kuri'u dubu 65

Jirgin ya tashi ne daga filin jirage na Murtala Mohammed, Legas ta filin Malam Aminu Kano da ke Kano a daren ranar Lahadi ya kuma dira filin Sarki Abdul-Aziz, Jeddah a Saudiyya, rahoton Daily Trust.

Amma abin mamaki ga ma'aikatan jirgin, Hukumomin Saudiyya suka sanar cewa an soke bizar dukkan fasinjojin.

Hakan na zuwa ne duk da cewa dukkan fasinjojin an musu bincike na APIS a Najeriya kafin su taso kuma jami'an Saudiyya suna sa ido a kai.

Matakin da ofishin jakadancin Najeriya a Saudiyya ya dauka kan lamarin

Wata majiya daga ofishin jakandancin Najeriya da ke Jiddah ta ce jami'an shige da fice na Saudiyya sun ce ba su san wanda ya soke bizan ba amma an soke shi ne bayan jirgin ya riga ya kama hanya zuwa Jeddah.

Hukumomin na Saudiyya sun rage adadin fainjojin da za su dawo gida daga 264 zuwa 177 bayan ofishin jakadancin Najeriya ya saka baki a lamarin, This Day ya rahoto.

Kara karanta wannan

An garkame babban malamin addini a gidan yari kan zargin damfarar miliyan 305, bayanai sun fito

Jirgin yana hanyarsa na dawowa Najeriya dauke da fasinjojin da aka ki barinsu shiga Saudiyya; galibinsu masu zuwa aikin Umrah ne.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164