Israila Ta Fara Maganar Tsagaita Wuta Bayan Kashe Mutane Kusan 10, 000 a Falasdin

Israila Ta Fara Maganar Tsagaita Wuta Bayan Kashe Mutane Kusan 10, 000 a Falasdin

  • Yakin Israila da ‘Yan Hamas ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 10, 000 tun daga farkon Oktoba zuwa yanzu
  • Ganin kashe-kashen da ake yi, kasashen Larabawa sun tausayawa Falasdin, sun bukaci Israila ta hakura da zubar da jini
  • Gwamnatin Israila ba ta da niyyar hakura, ko da za ayi hakan, Benjamin Netanyahu ya ce wajibi a sako Yahudawa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Gaza - Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta shaida cewa akalla mutane 9, 770 su ka mutu bayan barkewan yakin Israila da dakarun Hamas.

Al Jazeera ta ce daga 7 ga watan Oktoba zuwa yanzu, mutum kusan 1, 000 wanda akalla 4, 800 daga cikinsu yara ne, sun mutu a Falasdin.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini ya bayyana mafita 1 tak ga matsalolin Najeriya

Israila
Israila ta kashe mutane 9, 7000 a Falasdin Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Israila: Yunkurin kasashen Larabawa

AP News ta ce an gaza cin ma matsaya tsakanin kasashen Larabawa da Antony Blinken a madadin Amurka kan dakatar da zubar da jini.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana haka sai aka ji Firayim Ministan Israila, Benjamin Netanyahu ya na nuna yiwuwar a tsagaita, The Jerusalem Post ta kawo rahoton.

Firayim Ministan Jordan, Ayman Safadi ya ce Larabawa na so a dakatar da yakin, amma Gwamnatin Israila ta ce ba za ta sararawa Gaza ba.

Israila za ta daina kisa a Falasdin?

Benjamin Netanyahu ya ce babu ta yadda Israila za ta yadda a sasanta alhali ba a dawo da Yahudawanta da ke tsare a hannun Hamas ba.

Mista Netanyahu ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci dakarun sojojin sama a Kudancin Isrila, ya aika jawabi ga abokai da makiyansa.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Najeriya, Isra'ila da sauran kasashen da Amurka ba ta da jakadu da kuma dalili

Jawabin Benjamin Netanyahu a Israila

"Ina kuma son in sanar da ku cewa wani abin da ba za mu yarda mu yi ba shi ne - babu tsagaita wuta ba tare da an dawo da ribatattu ba.
Dole a ajiye wannan batun daga tattaunawar.
Mu na fadan wannan ga makiya da kuma abokanmu. Za mu cigaba (da yakin nan) har sai mun murkushe su (makiyanmu).
Ba mu da wata mafita dabam. Ina tunanin kowa ya fahimci wannan.

- Benjamin Netanyahu

Hamas ta kai hari a Israila

Ku na da labari Israila ta ce mutane wanda da-dama fararen hula ne fiye da 1, 400 Hamas su ka hallaka a harin 7 ga watan Oktoban bana.

Har gobe Sojojin Israila na kashe rayukan Falasdinawa da sunan dakarun Hamas sun kai masu hari a yankin kudancin kasar a watan jiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng