Isra’ila v Hamas: Kasa Daya Tilo a Latin Amurka da Ta Yanke Alaka da Isra’ila, Ta Fadi Dalili

Isra’ila v Hamas: Kasa Daya Tilo a Latin Amurka da Ta Yanke Alaka da Isra’ila, Ta Fadi Dalili

  • Yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas, kasar Bolivia ta dauki mummunan mataki kan Isra’ila
  • Bolivia ita ce kasa ta farko a Nahiyar Amurka da ta fara yanke alaka tsakaninta da kasar Isra’ila kan hare-haren ta’addanci kan Gaza
  • Wannan matakin na Bolivia na zuwa ne yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai farmaki Gaza tare da hallaka kananan yara a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kasar Bolivia ta zamo kasar Nahiyar Amurka daya tilo da ta yanke alaka da Isra’la saboda hare-haren ta’addanci kan Gaza.

Gwamnatin Bolivia ta kirayi tsagaita wuta tare da bukatar bude kofofin kai agaji yankin Gaza da ke shan hare-hare, cewar Reuters.

Kara karanta wannan

"Ina da bidiyo" Sanata ta tona asirin gwamnan arewa, ta faɗi yadda ya yi yunƙurin kashe ta

Bolivia ta yanke alaka da Isra'ila saboda hare-hare kan Gaza
Kasar Bolivia ta dauki mataki kan Isra'ila. Hoto: Luis Arce, Benjamin Netanyahu.
Asali: Facebook

Wane mataki Bolivia ta dauka kan Isra’ila?

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar, Freddy Mamani ya bayyana cewa sun dauki matakin ne don nuna kin amincewarsu da hare-haren Isra’ila kan Gaza.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci bude duk wasu kofofi da kasashe za su kai taimakon gaggawa Gaza musamman ruwa da wuta, cewar Arise TV.

Wannan mataki na Bolivia na zuwa ne yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare da ke sanadin rayukan mutane a Gaza.

Wane martani Isra'ila ta yi kan Bolivia?

Kasar Isra’ila ta soki matakin na Bolivia inda ta ce wannan mika kai ne ga ta’addanci.

Isra’ila ta zargi Bolivia da hada kai da ‘yan ta’addan kungiyar Hamas da ke kai hare-haren ta’addanci kan Isra’ila.

Har ila yau, shugaban kasar Chile, Gabriel Boric ya umarci dawo da jakadan kasar da ke Tel Aviv na Isra’ila inda ya soki hare-haren Isra’ila kan Gaza.

Kara karanta wannan

Atiku: Kotun koli ta halasta haram da kirkirar takardar bogi

Haka shi ma shugaban Colombia, Gustavo Pedro ya dauki irin wannan mataki na Chile.

Gumi ya bude asusun ba da taimako ga Falasdinu

A wani labarin, Sheikh Ahmed Gumi ya bude asusun taimakon Falasdinu don taimakawa ‘yan uwa da ke cikin mawuyacin hali a yankin.

Gumi ya bayyana haka ne yayin wani karatu da ya yi a masallacin Sultan Bello da ke birnin Kaduna inda ya nemi hadin kan Musulmi.

Wannan mataki na Gumi na zuwa ne yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren ta’addanci kan Gaza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.