Iran Ta Gargadi Isra'ila Kan Shirinta Na Mamaye Zirin Gaza
- Yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin isra'ila da Hamas, Iran ta yi gargadi ga kasar kan mamayar Gaza
- Ministan harkokin wajen Iran, Hossien Amir-Abdollahian ya bayyana haka yayin da sojin Isra'ila su ka shirya mamayar Zirin Gaza
- Wannan na zuwa ne bayan harin ramuwar gayya da Isra'ila ta kai kan kungiyar Hamas a ranar Asabar da ta gabata
Gaza, Falasdinu - Kasar Iran ta gargadi Isra’ila kan shirinta na mamayar yankin Zirin gaza yayin da ake ci gaba da gwabza yaki.
Iran ta ce muddin su ka kuskuri mamayar Gaza, za su marawa Falasdinu baya da daukacin kasashen Gabas ta Tsakiya, cewar Al-Jazeera.
Meye Iran ke cewa kan Isra'ila na mamayar Gaza?
Ministan harkokin wajen kasar, Hossien Amir-Abdollahian shi ya bayyana haka yayin da sojin Isra'ila su ka shirya mamayar Zirin Gaza inda su ke jiran umarni daga magabatansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojin Isra'ila sun shirya mamayar Gaza don murkushe sojin kungiyar Hamas gaba daya a kankanin lokaci yayin da ake ci gaba da gumurzu.
Wannan na zuwa ne bayan kai hare-hare da ake tsakanin kungiyar Hamas da Isra'ila wanda aka shafe kwanaki ana yi.
Mutane nawa su ka mutu a rikicin Isra'ila da Falasdinu?
Rahotanni sun tabbatar da cewa akalla mutane fiye da dubu biyu su ka rasa rayukansu wadanda su ka hada da mata da kananan yara, The Jerusalem Post ta tattaro.
Har ila yau, mutane kusan dubu 10 sun samu raunuka sakamakon hare-haren da ake ci gaba da kai wa juna.
Hare-haren na zuwa ne bayan harin ramuwar gayyan da Isra’ila ke kai wa ta sama a Gaza, tun bayan farmakin da Hamas suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba.
Yakin Isra'ila/Falasdinu: Isra'ila Ta Yi Barazanar Datse Wuta, Ruwa da Fetur Kan Abu 1 Tak, Bayanai Sun Fito
Isra’ila ta ce akalla mutane dubu 1400 ne cikinsu har da sojoji 289 su ka mutu yayin hare-haren kungiyar Hamas a yankin.
Fasto ya goyi bayan Isra'ila a bidiyo
A wani labarin, Fasto Enoch Adeboye ya nuna goyon bayanshi ga kasar Isra'ila yayin da su ke ci gaba da yaki da Hamas.
Adeboye ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo inda ya ke addu'ar samun nasara ga kasar.
Asali: Legit.ng