Shehin Malamin Musulunci Ya Taba Hasashen Lokacin Da Daular Isra’ila Za Ta Rushe

Shehin Malamin Musulunci Ya Taba Hasashen Lokacin Da Daular Isra’ila Za Ta Rushe

  • Mansur Isa Yelwa ya tofa albarkacin bakinsa a game da dadadden yakin da ake yi tsakanin Israila da kasar Falasdinu
  • Malamin Najeriyan ya tuno da wata maganar malamin Falasdin da ya yi hasashen rushewar kasar Yahudawan a 2027
  • An kafa Israila ne a 1987, kafin ya rasu, Sheikh Ahmad Yasseen ya ce babu kasar da za ta yi fiye da shekaru 40 ta na iko

Bauchi - A wani karatu da ya yi, Mansur Isa Yelwa ya yi tsokaci game da abubuwan da ke faruwa tsakanin kasashen Israila da Falasdinu.

Sheikh Mansur Isa Yelwa a darasin da ya gabatar kamar yadda aka wallafa a shafin Twitter, ya ce alamun rushewar Israila sun tabbata.

Shehin ya ke cewa akwai malaman da hangen nesarsu ya nuna daular Yahudawan za ta kife, El-Uthman Zakariyya ya wallafa bidiyon.

Kara karanta wannan

Wike: Tashin Hankali Yayin da Tsohon Kakakin APC Ya Bukaci Tinubu Da Ya Kama Sheikh Gumi

Daular Isra’ila
Israila ta kai wa Falasdin hari Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Hasashen Sheikh Ahmad Yasseen a kan Israila

Malamin ya ce Marigayi Sheikh Ahmad Yasseen ya taba yin hasashen cewa kasar Israila za ta ruguje nan da shekarar 2047 bayan ta balaga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Ahmad Yasseen ya rasu ne a shekarar 2004 a sakamakon bam da ya fado a kan shi, hakan ta sa aka yi masa sallar gawa a Saudiyya.

Dole nan gaba kasar Israila za ta rugurguje

Farfesan ya ce malamin ya taba fadawa Aljazeera a shekarar 1999 cewa daular Israila za ta cika wa’adin da Allah (SWT) ya yanke mata a duniya.

A ra’ayin Ahmad Yasseen, sai muzgunawar da Israila ta ke yi wa Falasdina ya yi kamari, sannan karfin kasar zai ragu, sai a daina labarinta.

Yayin da ta ke cikin ganiyarta, malamin ya ce abokiyar gabarsu za ta gawurta a duniya bayan da farko ba ta kai matsayin da ta ke kai ba.

Kara karanta wannan

Ba Za Ayi 8 ba: Gumi Ya 'Tona Asirin' Gwamnatin APC, Ya Nuna Tinubu ba Zai Zarce ba

Kamar yadda jariri ya ke fara rayuwa da rauni har ya isa shekaru 40, daga nan karfinsa ya ragu, haka Yasseen ya ce dauloli su ke rayuwa.

Yadda Israila ta fara yin karfi a tarihi

"Abin da mu ka fahimta a Al-kur’ani, shekaru 40 ne kurewa na karfi. Duk wata kasa da za ta yi karfi, za ta yi shekaru 40 ne
Daga nan kuma sai a samu wata da za ta gaje ta saboda Allah SWT bai yi alkawarin akwai wata kasa da za ta dawwama ba."

- Sheikh Mansur Isa Yelwa esq.

Daga 1947 zuwa 1987 Israila ta rika rarrafe, bayan nan ta fara mamaye Falasdina, daga 2027 kuma Sheikh Yasseen ya ce kasar za ta ruguje.

Harin Hamas a kan Israila

A makon jiya aka samu rahoto da ya bada mamaki, kwatsam aka ji kungiyar Hamas mai rajin kare Falasɗinawa ta kai hare-hare a kan Isra'ila.

Rundunar sojin Isra'ila ta tabbayar da aukuwar harin da ba ta ta taba tsammani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng