Yakin Isra'ila da Falasdinu: Jerin Yan Kasashen Wajen da Suka Mutu, Bace, Aka Sace

Yakin Isra'ila da Falasdinu: Jerin Yan Kasashen Wajen da Suka Mutu, Bace, Aka Sace

Rikicin da ake cigaba da gwabzawa tsakanin Isra'ila da ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinu ta Hamas, ya yi sanadin mutuwar ƴan kasashen waje da dama, wasu an bayyana ɓacewarsu yayin da aka yi garkuwa da wasu.

A cewar Aljazeera, an tabbatar da mutuwar aƙalla baƙi ƴan ƙasashen waje mutum 54, mutum 65 kuma sun ɓace, yayin da wasu mutum 20 aka yi garkuwa da su, bayan harin bazata da mayaƙan Hamas suka kai wa Isra’ila a ƙarshen mako.

Rayuka da dama sun salwanta a yakin Isra'ila-Falasdinu
Yan kasashen waje sun mutu wasu sun bace a yakin Isra'ila-Falasdinu Hoto: @IsraelHamasWarr
Asali: Twitter

Rayuka da dama sun salwanta

Fiye da mutum 1,500 ne suka mutu a cikin kwanaki uku da Hamas ta ƙaddamar da hari a kan Isra'ila, a cewar Financial Times.

Ga jerin ƴan ƙasashen waje da aka kashe, suka ɓace ko aka sace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

A Karo Na Uku, 'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari, Sun Yi Garkuwa da .Ɗaiban Fitacciyar Jami'ar Arewa

  • Argentina: Mutum bakwai sun mutu, 15 sun ɓace
  • Austria: Mutum uku sun ɓace
  • Brazil: Mutum uku sun ɓace
  • Cambodia: Mutum daya ya mutu
  • Canada: Mutum ɗaya ya mutu, uku sun ɓace
  • Chile: Mutum biyu sun ɓace
  • Colombia: Mutum biyu sun ɓace
  • Faransa: Mutum biyu sun mutu, 14 sun ɓace
  • Jamus: An yi garkuwa da su da dama
  • Ireland: Mutum ɗaya ya ɓace
  • Italiya: Mutum biyu sun ɓace
  • Mexico: An yi garkuwa da mutum biyu
  • Nepal: Mutum 10 sun mutu, ɗaya ya ɓace
  • Panama: Mutum ɗaya ya ɓace
  • Paraguay: Mutum biyu sun ɓace
  • Peru: Mutum biyu sun ɓace
  • Philippines: Mutum bakwai sun ɓace
  • Rasha: Mutum ɗaya ya mutu, huɗu sun ɓace
  • Tanzania: Mutum biyu sun ɓace
  • Thailand: Mutum 18 sun mutu, an yi garkuwa da mutum 11
  • Ukraine: Mutum biyu sun mutu
  • United Kingdom: Mutum yaya ya mutu, daya ya ɓace
  • Amurka: Mutum 11 sun mutu, wasu sun ɓace

Kara karanta wannan

Mutanen Gari Sun Halaka Hatsabibin Ɗan Bindiga, Sun Kwato Muhimmin Abu 150 a Jihar Arewa

Shugaba Joe Biden a cikin wata sanarwa ya ce akalla ƴan ƙasar Amurka 11 ne suka mutu, ya kuma ce akwai yiwuwar ƴan ƙasar suna cikin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su.

Tsohon Minista Ya Magantu Kan Yakin Isra'ila-Falasdinu

A wani labarin kuma, tsohon ministan waje na Najeriya ya yi magana kan manufar ƙasar Isra'ila dangane da yaƙin da take da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu.

Farfesa Bolaji Akinyemi ya bayyana cewa Isra'ila so take yi ta kitsa yaƙin duniya ɓa uku ta hanyar haɗa faɗa tsakanin ƙasashen Amurka da Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng