Babu Abinci, Babu Lantarki, Israila Ta Toshewa Falasdinawa Hanyar Rayuwa
- Yoav Gallant ya dauki alwashin ganin bayan Falasdinawa ta hanyar toshe inda za su iya samun kayan abinci ko ruwa
- Ministan tsaron ya ce Israila ba za ta daga kafa ga mayakan Hamas ba, ya sha alwashin ganin bayansu a yakin da ake yi
- ‘Yan Hamas ta bakin Abdel-Latif al-Qanoua, sun yi alkawarin ceto duk wani musulmin da kasar Israila ta cafke shi
Gaza - Ministan tsaron Israila, Yoav Gallant ya bada umarnin a toshe Gaza ta yadda Falastina ba za ta samu wutar lantarki ko abinci ba.
Times Of Israel ta rahoto cewa dakarun kasar Israila za su rufe hanyar da kayan abinci, fetur ko lantarki zai su iya kai wa ga 'yan Gaza.
Dakarun Hamas ke da iko da zirin Gaza da ke iyaka da kasashen Israila da Masar.
A ranar Asabar da ta gabata, mayakan Hamas su ka mamayi Israilawa a wani mummunan hari da kasar ta ce ba ta taba ganin irinsa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana kashe Musulmai a Kudus
Shugaban rundunar Hamas, Mohammed Deif, ya ce sun kai harin ne saboda cin kashin da ake yi wa musulmai a masallacin alfarma a Kudus.
Mohammed Deif ya zargi sojojin Israila da hallaka mutanen Falasdina a duk shekara.
Za a toshe komai a Gaza
A makon nan ne Yoav Gallant ya yi alwashin za a rufe komai a birnin Gaza ta yadda za a rasa wutar lantarki, kayan abinci da kuma man fetur.
Gallant ya ke cewa a game da Hamas, su na yaki ne da dabbobi, dole sai sun yi da gaske. New York Times ta fitar da labarin nan a ranar Litinin.
Hamas za ta kubutar da Musulmai
Mai magana da yawun bakin sojojin Hamas, Abdel-Latif al-Qanoua, ya ce burinsu shi ne su ceto duk wani Bafalastine da yake hannun Israila.
Rahoto ya ce zuwa yanzu an kashe sojoji da mutanen Israila fiye da 700 kuma ana zargin akwai wasu mutane sama da 2, 150 da su ka jikkata.
A Gaza, akwai mutane 400 da ake zargin sun mutu yayin da rundunar Hamas ta ke cigaba da kokarin kamo mutanen Israila da ake yaki da su.
Za mu kawo karshen Hamas
Firayin Ministan Isra'ila a wani rahoto, ya yi alwashin ganin bayan daukacin dakarun 'Yan Hamas saboda farmakinsu a kan Isra'ilawa.
Yanzu haka daruruwan mutane sun mutu yayin da ake cigaba da yaki tsakanin Isra'ila da Falasdinawa da su ke kukan an gaje masu kasa.
Asali: Legit.ng