Sanatan Amurka Da Iyalansa Sun Mutu a Wani Mummunan Hatsarin Jirgin Sama
- Rahotanni sun ce wani Sanata da iyalansa sun rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a Utah ta jihar Arizona
- Sanatan na Datoka ta Arewa da matarsa da ƴaƴansu guda biyu sun mutu a hatsarin jirgin a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba bayan tsayawa shan mai
- Suna komawa gida ne bayan sun ziyarci danginsu a Scottsdale, Ariz, a cewar wata sanarwa da ƴan sanda suka wallafa a Facebook
Utah, Amurka - Wani ɗan majalisar dattawan Amurka a Arewacin Dakota, Doug Larsen, da matarsa da ƴaƴansa biyu sun mutu a hatsarin jirgin sama a daren Lahadi, 1 ga Oktoban 2023.
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa an tabbatar da mutuwar Larsen ne a ranar Litinin 2, ga watan Oktoba a cikin wani sakon email da shugaban masu rinjaye na majalisar dattijawa, David Hogue, ya aike wa takwarorinsa sanatoci.
Saƙon na cewa:
"Sanata Doug Larsen, matarsa, Amy, da ƴaƴansu biyu sun mutu a wani hatsarin jirgin sama a yammacin jiya a Utah."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar da ofishin Sheriff ya fitar a taƙaice na cewa:
"An kammala aikin ceto. Abin takaicin mutanen huɗu ba su tsira daga hatsarin ba. Za a ba da ƙarin bayani da zarar an sanar da ƴan uwansu." Cewar rahoton CBS NEWS.
An ba da rahoton cewa iyalan suna komawa Dakota ta Arewa daga ziyarar dangi a Scottsdale, Arizona. Sun tsaya don neman mai lokacin da jirginsu ya sauka a Utah.
A halin da ake ciki, ana kan binciken musabbabin hatsarin jirgin.
Muhimman bayanai game da sanata Doug Larsen
A cewar wani rahoto na New York Post, Larsen, ɗan Republican, an fara zaɓen shi ne a matsayin sanatan Dakota ta Arewa a shekarar 2020, inda ya jagoranci wani kwamitin da ya shafi dokokin masana'antu da kasuwanci.
Shi da matarsa, Amy, dukansu ƴan kasuwa ne. Ya kuma kasance Laftanal Kanal a rundunar tsaron ƙasa ta Arewacin Dakota.
Matukin Jirgi Ya Mutu Ana Tsaka Da GuduJirg
A wani labarin kuma, wani matuƙin jirgin sama ya ce ga garinku nan ana tsaka da tsala gudu a sararin samaniya.
Jirgin saman wanda ya taso daga Miami zuwa Chile yana ɗauke da fasinjoji 271, waɗanda gaba ɗayansu hankulansu sun tashi bayan mutuwar matuƙin.
Asali: Legit.ng