Shugaba Tinubu Ya Roki ’Yan Najeriya Da Ke Amurka Su Dawo Gida Don Kawo Ci Gaba
- Yayin da ya ke ci gaba da tattaunawa da ‘yan Najeriya a ketare, Bola Tinubu ya roke su da su dawo Najeriya
- Tinubu ya bayyana haka ne yayin da ya ke ganawa da ‘yan Najeriya a birnin New York na Amurka
- Ya ce a yanzu an samu ci gaba sosai a kasar inda ya bukace su da su manta da wahalhalun baya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
New York, Amurka – Shugaba Bola Tinubu ya roki ‘yan Najeriya da ke kasashen ketare da su dawo Najeriya.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin da ya ke ganawa da ‘yan Najeriya a birnin New York na Amurka.
Meye Tinubu ya roki 'yan Najeriya a Amurka?
Shugaban ya bayyana musu cewa a yanzu fa an samu ci gaba a najeriya za su iya dawowa don taimakawa a bunkasa tattalin arziki, Vanguard ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bukace su da su sauya tunani a kan Najeriya kamar a da, su zo kasar don amfana da bunkasar tattalin arziki da kuma damarmaki a kasar.
Ya ce:
“Zan ba ku misali daidai da ku, a baya na zauna a kasar waje, a irin halin da ku ke ciki, ku na bukatar sauya tunani wanda ya zama dole.
“Ku saka a cikin ranku a wannan dare, Najeriya gida ne da ke da damarmaki na kasuwanci masu yawa.”
Tinubu ya yi alfahari da irin ci gaban da ake samu a Najeriya ta bangarori da dama da ya jawo wa kasar ci gaba, cewar Tribune.
Wane alkwari Tinubu ya musu?
Ya bayana damar da ake da su yanzu a Najeriya inda ya bukace su da su zama masu ba da gudumawa a ko wane bangare.
Ya kara da cewa:
“Ina alfahari da ku ganin yadda ake yabonku da da’a yayin da ku ke zaune a wadannan kasashe.
“Amma, mu na bukatarku a gida, Najeriya ta iso inda ake bukata, ku manta da wahalhalun da su ka faru a baya, yanzu an samu sauyin shugabanci.”
Remi Tinubu ta roki ‘yan Najeriya a ketare su dawo gida
A wani labarin, Uwar gidan shugaban kasa, Remi Tinubu ta roki ‘yan Najeriya da ke kasashen ketare da su dawo gida.
Remi ta bayyana haka ne yayin taron bunkasa tattalin arziki a birnin York a ranar 18 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng