Akwai Yiyuwar Fara Biyan Kudi Ko Wane Wata Ga Masu Amfani Da Twitter, Elon Musk

Akwai Yiyuwar Fara Biyan Kudi Ko Wane Wata Ga Masu Amfani Da Twitter, Elon Musk

  • Akwai hasashen za a fara biyan kudade duk wata musamman ga masu amfani da shafin Twitter don rage amfani da shafukan bogi da ke yawo
  • Shugaban kamfanin Twitter, Elon Musk shi ya bayyana haka a jiya Litinin 18 ga watan Satumba yayin ganawa da Fira Ministan Isra’ila
  • Benjamin Netanyahu ya tambayi Musk yadda za su kare amfani da shafukan bogi a kamfani, inda Musk ya ce akwai yiyuwar fara biyan kudin

Isra'ila - Shugaban kamfanin Twitter da ta sauya suna zuwa X, Elon Musk ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za su iya kawo tsarin da masu amfani da Twitter za su fara biyan kudi duk karshen wata.

Musk ya fadi haka ne a a jiya Litinin 18 ga watan Satumba a lokacin da yake ganawa da Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Na Kusa da Atiku Abubakar Ya Tona Asirin Gwamnatin Shugaba Tinubu Kan Abu 1 Tal

Elon Musk ya ce za a fara biyan kudin amfani da Twitter duk wata
Elon Musk Ya Ce Za A Fara Biyan Kudi Duk Wata Ga Masu Amfani Da Twitter. Hoto: ABC News.
Asali: Getty Images

Meye dalilin fara biyan kudin?

Wannan na zuwa bayan Fira Ministan ya tambaya shi kan yadda zai magance matsalolin da ake samu na amfani da shafukan bogi wurin nuna wariya ga Yahudawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musk ya ce a kokarin shawo kan wannan matsalar a nan gaba za su fara karbar kudade duk wata ga masu amfani da Twitter, Telegraph ta tattaro.

Attajirin ya kawo sauye-sauye da dama tun bayan ya sayi kamfanin kan kudi har Dala biliyan 44.

A kwanakin baya, Musk ya bayyanan cewa shafin na Twitter ya yi asarar rabin kudin shigarsa ta hanyar tallace-tallace, cewar Sky News.

Rahotanni sun bayyana cewa ana samun shafukan bogi da mafi yawanci kwamfuta ke samar da su da kuma gudanar da su a madadin dan Adam.

Ya ce wasu na amfani da shafukan bogi wurin na nuna wariyar launin fata wanda hakan ke jawo rashin zaman lafiya a tsakanin al’umma musamman bangaren addini da kabilanci.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Innalillahi, Bene Mai Hawa 20 Ya Rushe Kan Jama'a a Babban Birnin Jihar PDP

Elon Musk Ya Dauko Sabon Gyara a Twitter Mai Amfani

A labarin makamancin wannan, shugaban kamfanin X wanda aka fi sani da Twitter, Elon Musk ya sanar da cewa zai kawo sabon fasali a madadin toshe juna da yanke alaka.

Musk ya kawo sauye-sauye a manhajar ta Twitter tun bayan sayan kamfanin a shekara 2021 kan kudi Dala biliyan 44.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.