Yadda Kada Ta Raba Wata Mata Da Kafarta a Rafin Baringo
- Winnie Keben ta koma mai.ƙafa ɗaya bayan tsautsayi y asanya kada ta cinye mata ƙafa a rafin Baringo da ke Kenya
- Matar ta bayyana cewa tun bayan da ta rasa ƙafarta rayuwa ta koma mata mai matuƙar wahala saboda halin da ta tsinci kanta a ciki
- Rafin na Baringo yana cike da kadoji saboda girman da ya ƙara a dalilin ruwan saman da ake samu wanda hakan ke kawo barazana ga mutanen da ke rayuwa a kusa da shi
Kasar Kenya - Wata mata ƴar ƙasa Kenya mai suna Winnie Keben ta bayyana yadda ta rasa ƙafarta a hannun kada a rafin Baringo.
Keben a wata hira ta musamman da BBC News Africa ta bayyana yadda ta rasa ƙafarta guda ɗaya bayan kada ta farmaketa a bakin rafin.
Rafin Baringo ya ƙara girma sosai
Rafin Baringo da ke ƙasar Kenya ya samu sauye-sauye da dama a cikin ƴan shekarun da suka gabata, inda ya ƙara girma sakamakon ruwan sama da ake samu sosai.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Masana sun bayyana cewa rafin ya ƙara girma inda girmansa ya ninka sau biyu a cikin shekara 10 da suka wuce, saboda ƙarin ruwan sama da aka samu a dalilin sauyin yanayi.
Wannan girman da rafin ya ƙara ya sanya mutanen da ke rayuwa a gefensa sun rasa matsugunansu, inda rafin duk ya mamaye su saboda girman da ya ƙara.
Girman da rafin ya ƙara ya sanya kadojin Nile suka cika shi maƙil, inda suke kawo barazana ga masu amfani da shi, musamman mutanen da ke kamun kifi a cikinsa.
Matan suna wanke kifayen da suka kamo a bakin rafin Baringo duk kuwa da hatsarin da kadojin Nile su ke da shi.
"Yadda kada ta cinye min ƙafa": Winnie Keben
A kalamanta:
"Nan da nan kawai kada ta cafke min ƙafa ta yi cikin ruwa da ni. Na yi ta ihu ina ɗago hannuna ta yadda mutane za su iya hango ni."
"Wani da yake a bakin rafin ne ya sanya adda ya ceto ni, amma kadar ta cinye min ƙafa."
"Tun da na rasa ƙafa ta, rayuwa ta kasance mai matuƙar wahala a gare ni, na koma ina dogara da wasu su yi min ƴan aikace-aikace ciki har da ɗebo ruwa."
"Yanzu na koma dole sai dai na saya ruwa, idan babu kuɗi kuma shikenan ba zan samu ruwa ba."
Magidanci Ya Shiga Halin Kakanikayi a Girgizar Kasa
A wani labarin kuma, Tayeb ait Ighenbaz, ya bayyana yadda ya tsinci kansa cikin halin ko dai ya ceto iyayensa ko ɗansa mai shekara 11 lokacin da suka maƙale a cikin ɓuraguzai lokacin girgizar ƙasa a birnin Marrakesh.
Tayeb tare da matarsa da ƴaƴansu biyu da iyayensa, suna gida a wani ƙauye na tsaunin Atlas lokacin da girgizar ƙasar.
Asali: Legit.ng