Girgizar Kasar Morocco: Magidanci Ya Bayyana Yadda Ya Tsinci Kansa Da Zabin Ceto Iyayensa Ko Dansa
- Wani mutumi ɗan ƙasar Morocco mai shekara 50, Tayeb ait Ighenbaz, ya bayyana cewa sai da ya yi zaɓi tsakanin ceto iyayensa ko ɗansa a lokacin girigizar ƙasa
- Tayeb ya yi bayanin cewa ya ceto ɗansa mai shekara 11 amma lokaci ya ƙure masa wajen ceto iyayensa waɗanda suka maƙale a cikin ɓuraguzai
- Mutane da dama sun rasu a girgizar ƙasa mai ƙarfin 6.8 da ta auku a birnin Marrakesh na ƙasar Morocco, a ranar Juma'a, 8 ga watan Satumba
Morocco, Marrakesh - Wani mutumi ɗan ƙasar Morocco, Tayeb ait Ighenbaz, ya bayyana yadda ya tsinci kansa cikin halin ko dai ya ceto iyayensa ko ɗansa mai shekara 11 lokacin da suka maƙale a cikin ɓuraguzai lokacin girgizar ƙasa a birnin Marrakesh.
A cewar BBC News, Tayeb tare da matarsa da ƴaƴansu biyu da iyayensa, suna gida a wani ƙauye na tsaunin Atlas lokacin da girgizar ƙasar ta auku a ranar Juma'a, 8 ga watan Satumba.
Sai da na zaɓa tsakanin iyayena da ɗana
"Komai ya faru cikin sauri. Lokacin da girgizar ƙasar ta auku, mu duka mun ruga zuwa wajen ƙofa. Mahaifina yana barci sai na kira mahaifiyata ta taho amma sai ta tsaya tana jiransa." A cewarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutumin mai shekara 50 wanda yake kiwon awakai ya bayyana cewa ya tsinci ɗansa da iyayensa maƙale cikin ɓuraguzai lokacin da ya dawo cikin gidan da ya ruguje.
Tayed ya bayyana cewa ya hango hannun ɗansa yana motsi a cikin ɓuraguzan, inda nan da nan ya fara ƙoƙarin ciro shi.
Ya yi bayanin cewa lokaci ya ƙure masa lokacin da ya koma wajen iyayensa waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin wani ƙaton dutse.
Idanunsa cike da hawaye ya bayyana cewa:
"Sai da na yi zaɓi tsakanin iyayena da ɗana. Na kasa taimakon iyayena saboda bangon ya faɗo kan fiye da rabin jikinsu. Abun akwai baƙin ciki. Na ga iyayena suna rasuwa."
Yaron wanda ya sanya hannayensa a jikin mahaifinsa, ya bayyana cewa:
"Mahaifina ya ceto ni daga mutuwa."
Tayeb ya bayyana cewa iyalansa sun koma yanzu suna rayuwa tare da ƴan uwansa a tantunan wucin gadi kusa da tsohon gidansu.
"Kamar a sake haihuwar mutum ne a cikin sabuwar rayuwa. Ba iyaye, ba gida, ba abinci, ba tufafi." A cewarsa.
"Shekara ta 50 yanzu, sannan na koma sai na sako daga farko."
Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru
A wani labarin kuma, adadin yawan mutanen da suka rasu a dalilin girgizar ƙasar da ta auku a ƙasar Morocco ya ƙaru da yawa.
Ministan harkokin cikin gida na ƙasar ya bayyana cewa adadin mutanen da suka rasu a sanadiyyar girgizar ƙasar ya kai mutum 2,497.
Asali: Legit.ng